Tsaro: Harkar na kawo ruɗani a Nijeriya

Assalamu alaikum, edita. Da fatan muna lafiya.

Harkar tsaro, wani rukuni ne daga cikin manyan rukunan gudanar da gwamnatin. Wanda hakan ya sa ake ware wa harkar maƙudan kuɗi don wanzar da zaman lafiya. Ko wace ƙasa da ta ke ikirarin cewa ta cika ƙasa, dole ne sai da samar da tsaron, domin kuwa idan babu zaman lafiya to babu gwamnati.

To irin hakan, wasu ƙungiyoyi da suka ɗaukar wa kansu tada zaune tsaye, sannan da hadafin cewa suna yaqi ne don nema yancinsu, ya sa matsalar tsaro ya haɗa dangi da siyasa. Duk da cewa, babban abinda ke haifar da saɓani a siyasa, akwai ƙabilanci. Ƙabilanci na ɗaya daga cikin abubuwan da suke haifar da rikicin siyasa, da kuma rashin zaman lafiya. Wanda ta wannan hanyar ne ke samu jam’iyyun adawa, da kuma ’yan bangar siyasa. Daga siyasa ne, sai kaga an haifar da rashin zaman lafiya. Domin kusan kowa yana anfani ne da hanyoyin da bai da kyau domin batacin ga abokin hamayyarsa. Daga anan ana iya zargin wasu ’yan siyasa na iya anfani da wasu miyagu don ɓata Gwamnati, da kuma nufin neman ’yancin don hamɓarar da gwamanatin.

Bayanai masu ɗaure kai

A koda yaushe, wannan fannin ta rashin tsaro, akwai bayanani da ya ke ɗaure wa mutane kai, wanda masu hankali daga cikin su suna buƙatar su san amsar tambayoyinsu. Kafin mu kai da nisa, daga cikin batun, zaka iya samun ko wanne Shugaban ’yan tawaye, ko ’yan ta’adda, zaka ga kowa na alamta tafiyar su da siyasa. Misali a Nijeriya, kwanaki an yi hirar da shugaban wani rukuni na ’yan bindiga da ke Jihar Zamfara, mai suna Bello Turji, ya yi ta ambatar siyasa siyasa a yayin da ake hira dashi. To, ta inane wannan siyasar ta shigo harkar tsaro. Mene ne alaƙar tsaro da siyasa. Me ya sa ’yan siyasa suna son su yi anfani da tashin hankali a harkokinsu, dama makamancin hakan wanda na ke son nayi magana akai.

A ƙasarmu Nijeriyya, harkokin tsaro abin ya fara zuwa da ruɗani, domin kusan maimakon a samu sauƙi abi sai ƙara ta’azzaza ya ke. Muna ganin Gwamnati na iya kawo ƙarshen abin amman har yanzu. Hakan ne ya sa Gwamnatoci da suka shuɗe muna ganin kamar basu iya aiki bane, ko wasu na zargin kamar da hannunsu a harkokin. Misali lokacin shugaba Godluck Ebele Jonathan, an yi zargin yana daga cikin masu taimaka wa Boko Haram, ko rura wutar rikicin, hakan ne ya sa ’yan ƙasar fushi tare da hanɓarar da mulkinsa, sannan Shugaba mai ci yanzu, Janar Muhammdu Buhari ya karɓa ƙarar. Kusan shima har yanzu kamar kwalliya ɓata biyan kuɗin sabulun.

Kamar yadda nace, harkar tsaro, harka ce da ake ware mata maƙudan kuɗaɗe, wanda wasu suna anfani da rikici da ake yi. Ba iya iyan siyasa kawai ba, abin zai iya zama harda jami’an tsaro wanda kusan su ne ƙashin bayan duk wata tashin tashina a a Nijeriya.

Mu duba maganar da Bello Turji yayi, na cewa wannan al’amarin akwai siyasa a ciki, duk da ma bai wani cikakken bayani game da ambata siyasa da ya yi a lamarin ba, amman maganan kusan haka ne. Misali wasu yan siyasa na anfani da wannan salon wajen cimma burinsu, haka zalika suma jami’an tsaro da nasu sakayi wajen tashin ko wane rashin tsaro. A maganar shi ya ambaci cewa, hakimai da sarakuna masu yi musu adalci wajen yin shari’a, wannan ya sa, idan aka yi ma mutum zalunci yau, gobe ma haka, akwana a tashi zaka ga zuciyar sa ta sauya suwa wani harkar daban, kaga rashi adalci jami’an tsaro na iya sababba rashin tsaro tare da rura wutar rikici.

Rashin sa ido

A wannan ɓangaren, bayan rashin adalcin jami’an tsaro akwai batun rashin sa ido ga abinda ke faruwa. Misali idan aka ce, tau bam ya tashi, kamata ne ace jami’an tsaro sunyi bincike mai kyau, a ina ake ƙera wannan bam ɗin, me dame aka yi anfani da shi. Idan kuma bindiga ne ko alburusai ne masu tada zaune tsaye suka yi anfani da shi, a yi bincike don a gano, wane kasa ce ke ƙera irin wannan makamai. Sannan Gwamnati na daga cikin tsare ƙasar ta, don ta bibiyi ya aka yi wannan makamin ya shigo Nijeriya, domin idan kuwa bincike ya kai bincike, Gwamnati da ikon tuhar ƙasar da ta yi wannan muƙamin.

Misali, an kama bindiga ƙirar AK57, ko AA, ko makamancin hakan, yana da kyau gwamnatin da jami’an tsaron ta su yi bincike akan ta ya wannan ya shigo hannun masu tada zaune tsaye a Nijeriya.

Wani abin ruɗani shi ne, zamu iya cewa Gwamnati na iya ƙoƙarin ta wajen sa ido da abubuwan da ke shiga da fice a ƙasar, domin kusan ta ko ina akwai jami’an tsaron ta masu bincikar sako sako na tigunan ƙasar. Kaduna ba aboda ta ke ba, amman ta ina ’yan bindiga suka samu daman zuwa titin Abuja zuwa Kaduna?

Babu wani fanni da ake kashe ma kuɗi kamar harkar tsaro. Sannan ko wane abu idan yana faruwa ya kamata a san mene ne hadafin kafuwar wannnan abin. Dalilin haka wasu na da buƙatarsu san cewa, ya aka yi irin wanna rashin tsaron ke faruwa? Me ake nema, ina ake son a cimma buri, sanna ta ina za a bi don samar da zaman lafiya. A wannan fannin mutane da yawa suna ganin gazawar jami’ai da kuma Gwamnati, wajen aiwatar da kwakwarar bincike don gani inane mafarar abin, kuma ina za a kwana. Wani lokacin ma jami’an tsaro na kawar da fushin su kan wani wanda bai yi laifi ba, hakan na biyowa bayan yadda abinda suke buƙata ba su samu ba. Kamar misali, suna buƙatar kayan yaqi, kayan wanzar da zaman lafiya, to sai kaga wasu sun riƙe, bai je gare su ba, hakan sai su sauya akalar tafiyar.

Ta ina ake shigo da makamai?

A kullum ana shigo da komai ƙasar, wani abin tambaya a nan shine ta ina ake shigo da su? Gwamnati ta san masu sana’ar sayar da makamai, me yasa ba za a iya tuhumar su da ɓata ƙasa ba? Gwamnati ta san masu ƙera wannan makaman, to ai tasan wajen ’yan ta’adda ke samun makamai. To me ya sa Gwamnati ba zata tsare ƙasarta ba?

Yanzu lamarin na hare-hare, ƙara ƙaruwa ya ke, Ƙungiyar Boko Haram sai sake mamayar ƙasar su ke. Misali da iya yankin Borno da Yobe da Adamawa kawai aka san da hare-haren ƙungiyar. Duk da a shekarun baya sun shiga Darazo yankin Bauchi, da kuma Kano, amman tin 2014 abin ya sauƙaƙa. Sai yanzu, a wannan shekara, baya-bayan nan, hare-haren mai kama da nasu, wanda suma sun ɗauki alhalin kai harin ya fara samuwa a Jihohin Kaduna da Kogi. An kai harin jirgin ƙasa, sun kuma ɗauki alhaki. Haka zalika an kai wani hari jihar Kogi, shina sune da alamun su suka kai hare-haren. Yanzu idan abin ya tabbada da cewa su ne ke wannan aika-aikan, kenan da sauran rina a kaba. Ƙasar za ta cigaba da fuskantar rashin zaman lafiya.

Idan irin wannan zai cigaba da faruwa, tare da mamaye garuruwa ya ƙasar za ta kasance? Sannan mene ne mafita a wannan lamarin, wane hanya za a bi wajen ganin an kawo ƙarshen rashin tsaro. Allah ya kawo mana mafita, ya ƙara tsare mana ƙasarmu Nijeriya.

Saƙo daga Mohammed Albarno. O8034400338, [email protected].