Abinda ya sa hukuma ta garƙame dukkan sassan Bankin Zenith a Owerri

Daga AMINA YUSUF ALI

Wata kotu ta umarci a garƙame dukkan rassan ɗaya daga cikin manyan Bankuna Nijeriya wato Bankin Zenith. Kuma ta nemi bankin da ya warware harƙallar Naira biliyan 1.9 da take zargin su da yi.

A cikin watan Mayun da ya gabata ne dai aka wayi gari da ganin wasu jami’an tsaro sun rufe tare da kange dukkan rassan Bankin Zenith da suke a garin Owerri a jihar Imo. Hakan ya biyo bayan umarnin kotu da ta nemi jami’an da su aikata hakan don ladabtarwa ga bankin.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan rufe bankin umarnin kotun masana’antu ce ta bada sakamakon wata ƙara da take da alaƙa da mataimakin gwamnan jihar Imo, Eze Madumere. Saboda almundahanar da mataimakin gwamnan yake zargin an yi masa ta Naira biliyan 1.9.

Hakazalika, rahotanni sun bayyana cewa, wannan hukuncin bankin ya sanya ma’aikata da masu ajiyar a bankin cikin halin ƙaƙa-nika-yi.

Wannan al’amari ya jawo al’amura su tsaya can a bankin. Hakan ya sa masu ajiya a bankin suke kukan cewa, an rufe musu manhajar hada-hadar bankin da take a kan wayoyinsu tun a ranar 29 ga Mayu zuwa yau. Hakan ya sanya suna shan baiwar wahala matuqa wajen turawa da fitar da kuɗi a asusun ajiyarsu ta hanyar amfani da manhajar ko yanar gizo na bankin Zenith.

A yanzu haka dai ana zargin a dalilin haka fiye da ma’aikata da dama ne suka rasa ayyukansu a Bankin a cikin watan Mayu.