Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Zaven fidda gwanin jam’iyyar APC mai gwamnatin tsakiya ta Nijeriya ya fi tsanani a siyasance tsakanin waɗanda a ke ganin ‘yan gida ɗaya ne wato uban APC Bola Ahmed Tinubu wanda ya lashe zaɓen da kuma mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo wanda ɗan gidan Tinubun ne.
Yanda Tinubu ya lashe zaɓen da tura Osinbajo a matsayi na uku ya sa tamkar ƙarfin da, da uban gida daban ne. Tun a kamfen ɗin neman zaɓe, Tinubu ya furta cewa babu ɗan sa da ya yi ƙarfin da zai iya takarar shugaban ƙasa. A filin taron wanda dandalin EAGLE a Abuja an ba da dama ‘yan takarar 23 su yi bayani kafin tafiya jefa ƙuri’a. An samu ‘yan takara 9 da su ka janye su ka ce sun miƙa wuya ga Tinubu. Cikin waɗanda su ka aikata hakan har da gwamnan Ekiti Kayode Fayemi da tsohon gwamnan Ogun Ibikunle Amosun.
Hatta matasan ‘yan siyasa irin Dimeji Sabur Bankole wanda ya zama kakakin majalisar wakilan Nijeriya ya na mai shekaru 37 ya janye kuma ya nuna ya bi dattawa ko lokacin ja da dattawa bai yi ba. A haka a ka yaɗa raɗe-raɗin in Osinbajo ya zo jawabi zai sanar da janye takarar ya marar baya ga Tinubun. Lamarin sam ba haka ya kasance ba don Osinbajo ya yi bayanai ne na irin abubuwan da gwamnatin Buhari ta cimma da kuma ya ke ganin ya na da ƙwarewar da zai jagoranci Nijeriya zuwa tudun mun tsira.
Osinbajo ya ce ya na nan daram a takarar kuma ya na buqatar goyon baya. Wasu daga mahalarta taron sun zagaye dandamalin jawabin su na sowar nuna goyon baya ga Osinbajo. An ga dillalan kamfen ɗin sa na karaɗe fili aƙalla wasu daga cikin su da irin ‘yan hula ‘yar kit da Osinbajo kin kifa kan goshi su ke sanye da ita da alamun su na tunanin samun nasara. Ba nan ba kawai sassan Abuja na cike da manyan alluna ɗauke da hotunan Osinbajo da nuna shi ne gwani na gwanaye da zai iya tsamewa ‘yan Nijeriya kitse a wuta. Fili ya cika da tunanin komai ka iya faruwa duk da yawan ‘yan takarar da su ka janyewa Tinubu.
Jawabin shugaba Muhammadu Buhari ya ƙara fayyace fatar gudanar da zaven bisa tsanaki da canko wanda wakilan zaɓe ke ganin zai iya lashe babban zaɓe cikin sauqi. Shugaba Buhari ya nuna fargabar matuƙar APC ta yi saƙo-saƙo har PDP ta kwace ragama to za a mayar da hannun agogo baya a abun da ya zayyana da nasarorin da gwamnatinsa ta cimma masu yawan gaske. Shugaban ya ce wasu ‘yan Nijeriya na da saurin mantuwa kan abubuwan da su ka faru gabanin zuwan gwamnatin sa kan mulki a 2015.
Ya kawo misalan gangar mai a kasuwar duniya ta kai dala 100 don haka PDP ta yi danasha da kuɗi a tsawon shekaru 16 kan mulki. Hakanan shugaban ya kawo batun illar Boko Haram da ya ce su na riƙe da wasu qananan hukumomi kafin zuwan gwamnatinsa amma yanzu an samu sauƙi. Duk da dai shugaban bai kawo batun ‘yan bindigar da su ka ɓulla a zamanin mulkinsa su na sacewa da kashe mutane ba, ya nuna gwamnatin sa ta yi duk abin da ya dace wajen inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
Da wannan shugaba Buhari ya ke son duk wanda jam’iyyar sa za ta tsayar takara sai ya zama mai jajircewa kan muradun yaqi da cin hanci da inganta tsaro kazalika da raya tattalin arziki. Shugaban ya yi bakin ƙoƙari wajen ƙaucewa nuna ya na da gefen da ya ke marawa baya a zaɓen fidda gwanin. Bayan kammala jawabin da zama jim kaɗan sai ya shiga kwambar motocin sa da rakiyar baburan jami’an tsaro ya koma fadar Aso Rock.
A gaskiya za a iya cewa an samu raguwar ƙarƙashin jama’a a tarukan da shugaba Buhari ya ke halarta. A baya fili ya kan yi kamar zai dare in shugaba Buhari ya shigo amma yanzu sai ka ga mutane na harkokin su da kaucewa inda jami’an tsaro za su kora su can baya don kar su zama barazana ga da’irar da shugaban ƙasa ya ke zaune wacce ta kai girman filin ƙwallo kuma cikin gilashi da harsashi ba ya hudawa.
Abin da na lura da shi a inda na rakuɓe tsakanin ‘yan jarida shi ne murnar da su ke yi kafin shuagaban ya iso taro da murnar da su ke ƙara yi in ya zo ficewa daga taron. Wannan kuwa ba wani dalili ne da ya wuce yadda jami’an tsaron shugaban kan zo da na’urar tsaida aikin yanar gizo da hakan kan hana manema labarun aikin su cikin sauƙi.
Bayan shafe dare da kusan rabin wuni a na kaɗa ƙuri’a da kidayawa sunan Tinubu ne ya ke ta amo ba ƙaƙƙautawa. Za a jera takardu da dama a na kiran sunan Tinubu kafin can ka ji an ce Amaechi ko Osinbajo. Gaskiya ba a ma je ko tsakiyar kaɗa ƙuri’a ba da a ka riƙa samun tsaiko sai da a ka fahimci Tinubu ya lashe zaɓen da zarra mai yawa.
Magoya bayan sa sun yi ta tsalle da kusan birgima a kasa don shiga yanayin farin ciki marar misali a salon zubar da ruwa a ƙasa a sha. Wannan fa ba babban zaɓe ba ne ballantana a yi tsammanin murna ce cikakkiya ta darewa madafun iko. Masu sharhi na cewa ko a haka a ka tsaya an cimma raguwar tankiya da zullumi a batun mulkin karɓa-karɓa tsakanin arewaci da kudancin Nijeriya.
Ko a filin Yarbawa na nuna godiya ga ‘yan Arewa don mara mu su baya da su ka yi. Mara bayan ya yi qarfi ne da matsayar da gwamnonin APC na arewa su ka ɗauka ta tura mulki kudu a babban zaɓe mai zuwa. Wannan lokaci ne mai muhimmanci da Nijeriya ke buƙatar haɗin kai don kange ƙasar daga miyagun muradun ‘yan aware. Ko a yanzu masu neman ɓallewa su kafa ƙasar Biyafara a Kudu maso gabashin Nijeriya da ke da akasarin ‘yan ƙabilar Ibo na nan na zubar da jinin waɗanda ba su yi mu su laifin komai ba in ka ɗebe ƙiyayyar ƙabilanci da bambancin yanki ko addini.
Kwanakin baya kuma an samu wani ɗan bangar Yarbawa Sunday Igboho da ke ta da fitina da sunan neman kafa ƙasar Yarbawa ta Oduduwa. Hana samuwar baraka ta ɓangaren APC na da muhimmanci wajen yaƙi da wannan mugun muradi. Haƙiƙa dagewa da sai mulki ya zauna a arewa babban abun dubawa ne da zai iya haifar ƙalubalen tsaro a kudu maso yamma da hakan zai iya shafar rayuka da dukiyar musamman talakawa ‘yan arewa da ke zaune a can su na kasuwanci da sauran sana’o’in su.
Abin da ya faru ga ‘yan kasuwa a Sasha a Ibadan babban misali na yadda a kan wulaƙanta dukiya da ma kashe ‘yan arewa a kudu bisa wasu dalilan da za a iya magancewa. Nijeriya ai ta ishi ‘yan ƙasarsu yi kasuwanci, addini da ma duk lamuran yau da kullum daga Legas zuwa Maiduguri daga Sakkwato zuwa Yola ba tare da takura ba. Duk manyan biranen da ka shiga a Arewa kai har ma ƙauyuka sai ka samu Yarbawa da Ibo da dama na zaune su na harkokinsu. Wasu ma a Arewa a ka haifi kakanninsu ma don haka nan ne tarihinsu na haihuwa ya ke. In haka ne Ina ribar neman wargaza ƙasa don cimma burin wasu ‘yan ƙalilan da ba su san darajar zama tare ba?
Yanzu kallo ya koma babban zaɓen 2023 da yadda za a samu tasirin mataimakan shugaba daga yankunan da ke daya ɓangaren da ba nan ne ɗan takarar shugaba ya fito ba. Kamar babbar jam’iyyar adawa ta PDP daga kudu za ta canko mataimakin shugaba don ɗan takarar ta Atiku Abubakar daga arewa ya ke. APC za ta darje a ‘yan arewa ta fitar da mataimakin shugaba. Tuni tsarin da wasu su ka bijiro da shi ya ke neman zama kamar dokar da ba ta tsarin mulki shi ne na Musulmi da Kirista.
A na cewa sam ba a amince a zamanin nan a Nijeriya a samu shugaba da mataimaki na bin addini iri ɗaya ba. A tarihi an samu hakan inda marigayi Moshood Abiola ya tsaya takara da Babagana Kingibe kuma su ka lashe zaɓen amma dai an soke shi don haka ba a rantsar da su ba valle a yi tutiya da wannan misalin. Ko a zamanin soja an samu inda shugaba da mataimaki duk su ke addini ɗaya kamar misalin shugaba Buhari a mulkin soja da marigayi Tunde Idiagbon.
Kammalawa:
Babbar shawara ga ‘yan Nijeriya su riƙa duba cancanta ba son kai ba wajen zavar waɗanda za su yi jagoranci don gudun samun tumun dare. Ba sabon abu ba ne mutane su yi zaɓe amma daga bisani su dawo su na kokawa da takun wanda su ka zava ko da addininsu da qabilarsu ɗaya ne da shugaban. Mafita wayar da kan al’umma da la’akari da ilimi, ƙwarewa da sanin ya kamata wajen dafifi ga mara baya ga waɗanda su ka fito neman jagoranci ido rufe ko ido buɗe.