Sarki Sanusi ya kammala babban digiri a Landon

Spread the love

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya kammala babban digirin shi a fannin shari’ar musulunci daga Jami’ar London da ke Ingila.

A wani faifan bidiyo da ke yawo, an ga Sarkin cikin murna yayin da ake faɗa masa cewa binciken da ya gudanar yayi kyau babu gyara a ciki.

Sarkin ya fara karatun babban digirin ne lokacin gwamnan Kano Ganduje ya tsige shi daga sarautar Kano a shekarar 2020.

Sarkin yana da digiri na biyu daga Jami’ar Afirka da ke Sudan. In da ya yi karatu a fannin Fiƙihu da shari’ar musulunci a shekarar 1997.

By ukarofi