Sarki Sanusi ya nemi gwamnati ta ba shi damar shiga sahun masu ƙoƙarin warware rikicin Fulani

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi na II ya bayyana aniyarsa ta shiga rikicin Fulani da ake fama da shi a Nijeriya don kawo ƙarshen matsalolin da hakan ke haifarwa.

A lokacin da ya karɓi baƙoncin tawagar al’ummar Fulani na ‘Tapital Pulaku Njode Jam Nigeria’ a Fadarsa ranar Talata, Sarki Sanusi ya ce, lokaci ya yi da gwamnati ya kamata da samar da mafita ta dindindin ga rikicin Fulani a Nijeriya.

“Wannan zai yiwu ne matuƙar gwamnati za ta bani cikakken agaji wajen cimma manufata, saboda su na da iko da kuma abin da zai sanya salo na ya yi aiki, yayin da ni kuma zan samar da tsare-tsaren yadda zan tafiyar da shi.”

Sarkin ya kuma ce, “tabbas Fulani a Nijeriya sun fuskanci hare-hare, wariya, kashe-kashe da tarwatsa su da sace musu dabbobi. Baki ɗaya waɗannan ababen a Nijeriya aka yi su, sannan akwai buƙatar a yi wani abu don dakatar da yanayin.”

Ya ƙara da cewa, lallai akwai ɓata-gari acikin al’ummar Fulani waɗanda suka yi sanadiyyar sauya kyakkyawar shaidar da aka yi musu wanda hakan ya kai su ga halin da suka tsinci kansu a yau.

Sarki Sanusi ya ƙara da cewa wannan shi ne lokacin da gwamnati za ta haɗa hannu tare da su don samar da mafita musamman tsakanin Fulanin da manoman da kuma wuraren da aka san su na ayyukan ta’addanci.

A lokacin da ya ke magana, jagoran tawagar, Modibbo Jada wanda kuma shi ne Lamiɗon Adamawa da aka naɗa da jimawa, ya ce sun zo Fadar ne don taya Sarki Sanusi murnar dawowa karagar mulkin Masarautar karo na biyu.

Ya ce, “mafi yawancin mutanenmu a jije suke, kuma idan yau na ce wa matasanmu su zo nan, wannan Fadar ta yi mana kaɗan. Mu na da mambobi a baki ɗaya jihohin Nijeriya 36”, inji shi.

Ya ƙara da cewa, Sarki Sanusi ya na da matsayin da zai taimaka wajen dawo da martabarsu da asalin abin da aka san su akai da kuma gudummawar da su ke bayarwa ga ci gaban ƙasa.

By Babaji