Ƙudirin bai wa jami’an kiyaye haɗura bindigu ya tsallake karatu na biyu a majalisa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wani ƙudiri da ke neman a samar da jami’ai na musamman a Hukumar kiyaye haɗura, FRSC da kuma inganta ta ya tsallake karatu na biyu a Majalisar Wakilai.

Ƴan majalisa Abiodun Derin Adesida da Olaide Lateef Muhammed ne suka ɗauki nauyin ƙudirin don a yi gyara ga dokar FRSC da za ta bada damar samar da ‘Special Armed Squad’.

Haka kuma, ƙudirin ya ƙunshi inganta jami’ai da ke da muƙamin ‘Deputy Corp Marshall’ ta hanyar amfana daga ribar yin ritaya da kuma inganta harkokin gudanarwa na ayyukansu.

Sannan, ya ƙunshi a ba su iko na hana ababen da ka iya kawo tseko akan titina da kuma ayyukan wayar da kan al’umma game da amfani da titina.

Kazalika, majalisar ta amince da batun bai wa jami’an ƙarin na’urorin fasaha a bakin aiki wanda ɗan majalisa, Garba Ibrahim Muhammad ya ɗauki nauyi.

By Babaji