Nasarar murubuciya Han Kang a duniya: Ƙalubalen marubutan Arewa

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Har yanzu duniya na cigaba da tattaunawa tare da yabawa da nasarar da wata marubuciya ‘yar ƙasar Koriya ta Kudu mai suna Han Kang ta samu a Gasar Fitattun Mutane ta duniya, wanda aka fi sani da Nobel Prize, wacce a bana aka yi nazari kan Rubutun Adabi, yayin da littafinta mai suna ‘The ɓegetarian’ ya zama na ɗaya. Littafin da ya taɓa samun nasara a Gasar Man Booker International Prize a shekarar 2016.

Littafi ne da yake ɗauke da labarin wata mata Yeong-hye wacce ta yi wa cin nama tawaye, sai dai hatsi da ‘ya’yan itatuwa, sakamakon wani mummunan mafarki da ta taɓa yi na irin mugunta da ƙeta da ɗan’adam yake nunawa dabbobi da jinsinsa, ‘yan’adam. Tun daga sannan, wannan mata Yeong-hye ta shiga fuskantar ƙalubalen rayuwa iri-iri daga ‘yan’uwanta da abokan zamanta, wanda har ta kai ga ana yi mata kallon wacce ta samu taɓin hankali.

Littafin, ‘The ɓegetarian’ ba kawai yana magana ne kan mutane masu ƙauracewa cin nama ba, ya taɓo labarin yadda rayuwar mata take shiga faɗi-tashi daga mu’amalarsu ta cikin gida da ta waje, da kuma yadda haƙuri da jajircewa yake kai su ga matakin nasara.

Ita kanta marubuciyar wannan labari, Han Kang, wacce ta shafe shekaru 30 tana rubutun adabi ta fuskanci matsalolin rayuwa iri-iri, musamman a ɓangaren rubutu, inda ake tunanin babu inda rubutun ta zai je, ballantana har ta samu shahara, sannan kuma gashi ma littattafan ta da harshen Koriya take rubutawa. Kodayake shi wannan gwarzon littafin nata an fassara shi a harshen Turanci a shekarar 2015, kuma tun daga lokacin yake ɗaukar hankalin manazarta daga ƙasashen duniya. Har ta kai ga littafin ‘The ɓegetarian’, ya shiga cikin jerin fitattun littattafan adabi 100 na ƙarni na 21, wanda jaridar New York Times ta tantance.  

Ko da a wannan Gasar ta Nobel Prize ta 2024, an ce littafinta ba ya cikin fitattun da ake sa ran za su samu nasara, don ba a ma shigar da sunansa cikin waɗanda aka ware na kashin farko ba. Amma abinka da ƙaddara sai gashi an sake fito da shi har kuma manazarta da alƙalan gasar suka yarda babu shakka ya cancanta, bisa wasu dalilai da suka bayyana. Sannan marubuciyar ‘yar shekara 53 a duniya, ita ce ake ganin mafi ƙarancin shekaru a cikin sauran marubutan da suka fafata a gasar a wannan shekara, kuma ‘yar ƙasar Koriya ta Kudu ta farko da ta taɓa cin wannan gasa a tarihin ƙasar.

Manazarta da dama sun kushe tsarin littafin da salon fassarar da aka yi masa, inda suke ganin wacce ta mayar da littafin zuwa turanci ba ta ƙware sosai ba, kuma ba baturiya ba ce, don ba ta fi shekara 3 da koyon turanci ba. An fi sa rai kan fitattun marubutan Koriya, irin su Bae Suah da Ha Seong-Nan, waɗanda su ma suna da littattafai da aka juya zuwa turanci, kuma sun fi ta gogewa.

Kamar yadda J.K Rawling marubuciyar littafin almara na Harry Potter ta sha gwagwarmaya da ƙyama, inda aka riƙa nuna rashin iyawarta da gogewarta, haka ita ma Han Kang ta riƙa fuskanta, inda ake yi mata ganin sabuwar marubuciya, marar basira. Duk kuwa da kasancewar ta rubuta littattafai sun kai 13 kafin wannan.

Daga cikin darussan da nake ganin ya kamata marubutan mu na Hausa su ɗauka shi ne, su faɗaɗa tunanin su na tsayawa a iya gasannin cikin gida, irinsu Gasar Gusau Institute ko sauran gasannin gajerun labarai da na cibiyoyin raya al’adu da harsunan gida da ake shiryawa. Mu fara tunanin yin labarai masu inganci da za su iya gogayya da sauran gwarazan marubuta na Afirka da duniya bakiɗaya. Sannan mu riƙa neman ƙwararrun masu aikin fassara daga Hausa zuwa Turanci su fassara mana, da ingantaccen turanci, yadda zai iya shiga kowacce irin gasa. Mu ƙara ƙoƙari wajen sanin ƙa’idojin rubutu da hanyoyin inganta rubutun adabi, da zai zama kaɓaɓɓe a ko’ina. Kuma mu daɗa jajircewa, kada mu bari kushe ko ra’ayin wasu akan rubutun mu ya sanyaya mana gwiwa, kan burinmu na zama fitattun marubuta a duniya. Kuma mu sani, nasara ba ta zuwa mana daga zaune, dole sai mun ƙara dagewa, mun yi karatu sosai, mun yi bincike, mun tuntuɗi masana, kan ire-iren waɗannan gasa da ake yi a Nijeriya, a Afirka, da duniya. Kada gwiwar mu ta yi sanyi! 

Idan za mu iya tunawa, akwai marubucin adabi ɗan Afirka kuma ɗan Nijeriya, Wole Soyinka, da ya kasance na farko da ya samu wannan nasara a Gasar Nobel a ɓangaren rubutun adabi a shekarar 1986. Wa ya sani ko nan gaba a samu wani marubuci ko marubuciya daga Arewacin Nijeriya da zai iya samun shiga wannan gasa?

An fara Gasar Nobel Prize ne a shekarar 1901, wacce ake gudanarwa a ƙarƙashin Gidauniyar Nobel. An kafa gidauniyar ne domin yaba wa da gudunmawar da wasu fitattun mutane suka bayar ga cigaban rayuwar ɗan’adam, a ɓangaren binciken kimiyya, magunguna, tattalin arziƙi, zaman lafiya, da kuma adabi. Kowacce shekara ana zaɓar ɓangaren da za a yi nazari a kansa wajen fitar da gasar. Kamar yadda a bana aka waiwayi ɓangaren adabi. Alfred Nobel ɗan ƙasar Sweden, da ya ƙirƙiro da sinadarin dynamite, wanda ake haɗa bom da shi, shi ne ya kafa wannan gasa, bayan ya karanta labarin mutuwarsa a jarida, inda aka riƙa tir da la’antarsa, saboda abin da ya ƙirƙiro wanda ake amfani da shi wajen halaka ɗan’adam. ɗan jaridar da ya yi rubutun ya zaci shi Alfred Nobel ne ya mutu, alhalin wani ƙaninsa ne Ludɓig Nobel, ya mutu, ba shi ba. Sakamakon wannan rahoto da Alfred ya karanta ne, sai ya ƙudiri aniyar yin wani abu da zai kawo wa duniya cigaba, domin wanke kansa. Don haka ya sadaukar da wani sashi na dukiyarsa wajen tallafawa ayyukan bincike da rubuce-rubuce da za su kawo wa ɗan’adam da duniya cigaba.

Da fatan wannan ɗan gajeren sharhi zai ƙara zaburar da marubuta, na Hausa da Turanci, da muke da su a nan arewacin Nijeriya.

By ukarofi