Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPC) ya sanar da sauye-sauye ga hukumarsa da manyan jami’anta, tare da sauke Umar Ajiya da Oritsemeyiwa Eyesan daga muƙamansu na babban jami’in kuɗi.
A madadinsu, NNPCL ya naɗa Isiyaku Abdullahi a matsayin sabon mataimakin shugaban zartarwa na Downstream da Udobong Ntia a matsayin EɓC (Upstream).
Haka nan, Adedapo Segun, wanda ya kasance EVP (Downstream) an naɗa shi babban jami’in kuɗi.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta NNPC ta fitar a daren Larabar da ta gabata, ta ce naɗe-naɗen na da nufin inganta harkokin tafiyar da harkokin kamfanoni da kuma yadda ake gudanar da ayyuka, wanda hakan ke nuni da yadda kamfanin na NNPC ya jajirce wajen samun nasara na dogon lokaci a fannin makamashin Nijeriya.
“Hukumar NNPC ta yi farin cikin sanar da jerin tsare-tsare na naɗin shugabanni. Waɗannan sauye-sauyen suna nuna ci gaba da himma don inganta tsarin tafiyar da kamfanoni, inganta ayyuka, da tabbatar da samun nasara na dogon lokaci a ɓangaren makamashin Nijeriya.
“An yi manyan muƙamai masu zuwa: Mista Adedapo Segun an naɗa shi Babban Jami’in Kudi (CFO). Mista Segun ya taɓa zama mataimakin shugaban a Downstream, inda ya ba da gudummawa sosai ga ayyukan kamfanin na ƙasa,” in ji sanarwar.
Hukumar gudanarwar ta kuma miƙa godiyarsu ga Mista Umar Ajiya da Misis Oritsemeyiwa Eyesan bisa sadaukarwar da suka yi da kuma hidimar da suka yi wa NNPC Limited,” in ji kamfanin mai na ƙasa.
