Zulum na matuƙar ƙoƙari wajen kawo cigaba a Borno – Hon. Abdu Labaki

Spread the love

Daga GAMBO ISA

Shugaban ƙaramar Hukumar Shani a Jihar Borno, Alhaji Hassan Abdu Labaki ya yaba wa Gwamna Farfesa Baba Gana Umar Zulum kan ayyukan ci gaban jihar a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abuja cikin makon nan.

Abdu Labaki, ya zayyana wasu daga nasarorin da gwamnan ya samu a fannin walwalar ɗan Adam, ababen more rayuwa, inganta harka ilimi, tsaro, da dai sauransu.

Abdu Labaki ya bayyana cewa nasarorin da gwamnan ya samu sun haɗa da, tsare-tsare na ci gaba kamar gina sakatariyar kansiloli na zamani a Shani, gina gidaje a babban birnin jihar da tsarin gidaje na ƙananan hukumomi a ƙaramar hukumar da gina babbar kasuwar zamani a Shani.

Honorabul Abdu Labaki, ya ce gina manyan hanyoyi da titunan cikin gari, kasuwar zamani a ƙaramar hukumar Shani da kuma cikin ƙananan hukumomi 27 da babban birnin jihar tare da gina gadojin sama a Maiduguri babban birnin jihar.

Honorabul Abdu Labaki ya yaba da yaƙi ‘yan ta’adda da gwamnan ke yi ba dare ba rana, inda gwamnn ya sayi wa jami’an tsaro kayan aiki da suka haɗa da jami’an tsaron haɗin gwiwa CJTF domin yaƙar ‘yan ƙungiyar Boko Haram a jihar.

Labaki ya ce gwamnan ya taɓa ɓangaren marasa galihu da kuma ƙananan yara a yankin Shani da sauran ƙananan hukumomin jihar.

Honorabul Abdu Labaki ya yaba wa gwamna Baba Gana Umaru Zulum a aikin gina gidaje a ƙaramar hukumarsa da kasuwar zamani da sauransu.

Ya kuma shawarci matasa da su kasance jakadun yankin nagari a kodayaushe.

Ya buƙaci matasa da su yi biyayya ga dokokin tsarin mulkin ƙasa, su guji shan miyagun ƙwayoyi, su riƙa saurare da mutunta dattijai a cikin al’ummarsu ko yankinsu, kana su kasance masu dogaro da kawunansu.

Abdu Labaki ya shawarci dattawan yankin da su goyi bayan shirye-shiryen gwamnati wajen gina ƙaramar hukumar.

Hon. Abdu Labaki, ya ce salon jagorancin Gwamna Farfesa Baba Gana Zulum, na da alaƙa da ginshiƙin da mataimakin shugaban ƙasa na yanzu Sanata Kashim Shettima ya kafa.

Kazalika ya shawarci takwarorinsa shugabannin ƙananan hukumomi 27 da su fara gudanar da shirye-shiryen da suka dace na Gwamna Baba Gana Zulum tare da zama masu riƙon amana ga jama’arsu, domin suna sa ran samun ribar dimokuraɗiyya.

 Labaki ya kuma shawarci matasa, dattijai a cikin al’umma, musamman Shani da su yi wa kasa addu’a, ya kuma shawarce su da su kasance masu rikon amana, ya kuma jajanta wa al’ummar jihar Borno, gwamna da Shehun Borno kan bala’in ambaliyar ruwa da ta afku a Maiduguri kwanan nan ya bukaci masu hannu da shuni. daidaikun mutane Philomtropies don bayar da gudummawa ga wadanda bala’in ambaliyar ruwa ya raba da muhallansu kwanan nan.

Honarabul Abdu Labaki ya buƙaci mai girma gwamna Baba Umara Zulum da ya yi amfani da ikonsa wajen yin kira ga gwamnatin tarayya a ƙarƙashin ma’aikatar ayyuka ta tarayya da ta fara gina titin Biu-Shani-Gombe domin samar da ribar dimokuraɗiyya ga jama’a.

Ya kuma yaba da salon jagorancin mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima da shugabancin babbar jam’iyyar ta ƙasa ƙarƙashin Dr Abdullahi Umar Ganduje. 

Da ƙarshe ya jajentawa gwamnatin tarayya, gwamnatin jihar Borno, Shehun Borno, Shehu Garbai El-kanami da majalisar Jere kan waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a baya-bayan nan, ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni da su ci gaba da tallafawa waɗanda abin ya shafa.

By ukarofi