Mutane 500 sun amfana da tallafin cibiyar uwargidan gwamnan Kebbi a Kamba

Spread the love

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi 

Aƙalla mata da matasa ɗari biyar ne suka ci moriyar tallafin kayan sana’o’in hannu da kuma jari daga cibiyar uwargidan gwamnan Kebbi Hajiya Zainab Nasir Idris a ƙaramar Hukumar mulki ta Dandi.

Da take jawabi yayin buɗe cibiyar da Sulaiman Fanna Foundation (SUFAF) ta gina kuma ta sakawa Hajiya Zainab Nasare Nasir Entrepreneurship Center Kamba, uwargidan gwamnan ta ce sanin kowa ne yanzu gwamanti ba ta iya bai wa kowa aiki saboda haka ne ya sa aka ƙirƙiro irin waɗannan cibiyoyin koyar da sana’o’i domin mutane su koyi sana’o’i daban-daban don su dogara ga kawunansu har ma su bai wa waɗansu mutane ayyuka a ƙarƙashinsu.

Hajiya Zainab Nasare ta ja hankalin waɗanda suka ci moriyar wannan gidauniyar da su yi amfani da ilmin sana’o’in da suka samu da kuma jari wajen ciyar da kawunansu da ƙasa gaba ta hanyar amfani da kaya da kuma jarin da suka samu yadda ya kamata.

Ya kuma bayar da tabbacin ofishinta a ko da yaushe shirye ta ke da ta tallafawa duk wani shiri da zai kawo cigaba a tsakanin al’umma.

ɗan majalisar dokoki ta jihar Kebbi mai wakiltar ƙaramar Hukumar mulki ta Dandi kuma wanda ya assasa wannan gidauniyar, Honarabul Sulaiman Abubakar Fannah ya ya bayyana cewa wannan yana daga cikin alƙawurran da ya yi a baya lokacin yaƙin neman zaɓe kuma in Sha Allahu wannan somintaɓi ne saboda akwai waɗansu shirye-shirye na musamman don inganta rayuwar al’umma masalan dangane da abinda ya shafi sana’o’i don kowa ya dogara ga kansa da kuma gine-ginen makarantun Islamiyya da boko tare da gyara waɗansu da kuma tsare-tsaren ilmin manya maza mata na yaƙi da jahilci.

Kayan da aka raba dai sun haɗa kuɗin jari da buhunan gyaɗa da awaki, injinan sarrafa filawa da niƙa da na casa, kekunan ɗinki da na’ura mai ƙwaƙwalwa (Laptop) da babbar kwamfuta  (desktop) da sauran kayanta.

By ukarofi