Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Kula da Cibiyoyin Kiwon Lafiya a Matakin Farko ta ƙasa NPHCDA ta bayyana cewa gwamnati za ta fara yi wa mutane allurar rigakafin zazzaɓin cizon sauro a jihohin Kebbi da Bayelsa daga ranar biyu ga Disamba.
Yin hakan na daga cikin matakan da gwamnati ta ɗauka domin gamawa da cutar dake yaɗuwa kamar wutar daji kuma yake kashe mutane a ƙasar nan.
Shugaban hukumar NPHCDA Muyi Aina ya sanar da haka wa manema labarai a Abuja.
Aina ya ce za a yi wa yara ƙanana ‘yan ƙasa da shekara biyar allurar rigakafin kyauta a waɗannan jihohi.
Ya ce ma’aikatan lafiya za su riƙa bin mutane gida-gida, asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko dake waɗannan jihohin domin yi wa yara rigakafin cutar.
Aina ya ce gwamnati na da burin yi wa yara miliyan 1.5 allurar rigakafin cutar a waɗannan jihohi.
Ya ce baya ga allurar rigakafin gwamnati za ta haɗa da sauran matakan daƙile yaɗuwar cutar da suka haɗa da raba wa mutane gidajen sauro da bada magungunan cutar kyauta.
Aina ya ce gwamnati za ta yi haka ne tare da haɗin gwiwar UNICEF da WHO.
“Gwamnati na da burin ganin ta rage yaɗuwar cutar zuwa kashi 40 a Nijeriya nan da 2030.
Shugaban hukumar ya yi kira ga iyaye da masu kula da yara a waɗannan jihohi da su tabbatar sun miƙa su an yi musu rigakafin.
