Ƙudirin haraji: Masu zanga-zanga sun yi wa majalisa tsinke kan goyon bayan Sanata Barau

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu matasa ‘yan Arewa sun gudanar da zanga-zanga a ƙofar shiga majalisa a ranar Talata domin jan kunnen masu zagin Shugaban Majalisar Dattawa da Mataimakinsa, Sanata Barau Jibrin, kan yunƙurin da suke na mara wa ƙudurin dokokin haraji baya wanda Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aike majalisar.

Masu zanga-zangar dai na riƙe da kwalaye waɗanda aka yi rubutu a kansu da ke cewa, “ku rabu da Sanata Barau,” da “Sanata Barau mai kishin al’umma ne,” da “ku daina sukar Sanata Barau” da “Sanata Barau shi ne jagora a Arewa,” sai kuma “Sanata Barau shi ne Sardauna na wannan zamanin.”

Sanata Barau dai ya fuskanci suka mai ƙarfi daga wasu sassan Arewacin Nijeriya tun bayan gabatar da ƙudurin sake fasalin haraji wanda majalisa ta fara nazarinsa.

Mataimakin shugaban majalisar shi ne mai wakiltar Kano ta Arewa wanda ya jagoranci zaman majalisar da aka yi a ranar Laraba a lokacin da kwamitin kuɗi da sake fasalin haraji na fadar shugaban ƙasa ya bayyana a gaban majalisar suka domin yi wa majalisar ƙarin haske kan ƙudurorin.

A ranar ne kuma wasu daga cikin ‘yan majalisar, musamman sanata Ali Ndume daga jihar Borno da takwaransa, sanata Abdul Ningi, suka yi ƙoƙarin hana kwamitin kuɗin bayyana aka gaban majalisar.

Wannan al’amari ya jawo muhawara mai zafin gaske a majalisar wanda har wasu daga cikin ‘yan majalisu daga Arewa suka yi ƙoƙarin ficewa daga majalisar, amma daga baya suka fasa.

Sai dai har zuwa wannan lokaci, mataimakin shugaban majalisar bai fito ya bayyana ra’ayinsa game da wannan ƙuduri ba, duk da ana zargin cewa yana nuna goyon bayansa ne.

ƙudurin dokokin dai sun tsallake karatu na biyu a majalisar a ranar Alhamis inda aka miƙa ƙudurin ga kwamitin kuɗi na majalisar wanda sanata Sani Musa daga jihar Neja ke jagoranta domin cigaba da bin matakan da suka kamata kamar na jin ra’ayin al’umma.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya kuma ba da umarni ga kwamitin da ya shigo da majalisar tattalin arziƙin ƙasa da ƙungiyar gwamnonin Arewa da ƙungiyoyin fararen hula cikin taron jin ra’ayin al’umma. Har zuwa yanzu dai kwamitin bai sanya ranar da za a gudanar da taron ba.

Abin da masu zanga-zangar suka faɗa

Tijjani Mohammed wanda ya zanta da ‘yan jarida a madadin sauran masu zanga-zangar, ya ce, duk masu zagin sanata Barau kan ƙudurin dokin sake fasalin haraji maƙiyan Arewa ne.

Mohammed, wanda tsohon shugaban ƙungiyar ɗalibai ne na ƙasa (NANS), ya ce matasa a Arewa suna goyon bayan wannan ƙuduri na sake fasalin haraji.

“Bari na gaya maka, waɗanda ke sukar Sanata Barau a ‘yan kwanakin nan, maƙiyan Arewa ne, maƙiyan Nijeriya ne, maƙiyan ‘ya’ya da jikoki ne da za su zo nan gaba.”

“Mu ba ma adawa da waɗannan ƙudurori da suka haɗa da na sake fasalin haraji da duk abin da zai kawo wa yankinmu cigaba da ma ƙasa bakiɗaya,” In ji Mohammed.

Daga nan ne ya ƙarfafa wa Barau guiwa kan cigaba da wakiltar al’umma ta hanyar kare muradan Arewa tsakani da Allah. Sannan ya yaba masa kan ɗaukar nauyin ƙudurin samar da hukumar raya yankin Arewa maso yamma.

“Ya yi abin a yaba masa a majalisa. Shi ne sanatan da ya fi kowanne sanata a Arewa idan aka yi la’akari da ƙudurin samar da hukumar raya yankin Arewa.”

“Bari na gaya maka, idan aka magance rabin matsalolin da Arewa ke fama da su, kamar an magance rabin matsalolin da ke damun Arewa ne,” inji Mohammed.

By ukarofi