
Daga BELLO A. BABAJI
Aƙalla boma-bomai biyu ne suka tashi a wurare mabanbanta a yankin Ɗan-Sadau dake ƙaramar hukumar Maru ta Jihar Zamfara.
Rahotonni sun bayyana cewa ɗaya daga cikin boma-boman ya tashi ne akan hanyar dake tsakanin Ɗan-Sadau da Malamawa yayin da ɗayan ya fashe a hanyar Malele duk a gundumar ta Ɗan-Sadau.
Wani mazaunin yankin mai suna Nuhu Babangida ya ce wata babbar mota ɗauke da hatsi da fasinjoji, ta tsallake rijiya da baya a lokacin da ta gitta kusa da bom ɗin.
Ya ce a lokacin da boma-boman suka fashe a Malamawa da hanyar Malele, ba a samu asarar rai ko jikkata ba.
Wannan shi ne karo na uku da ake dasa bom a Ɗan-Sadau cikin sati guda.
Mutane 12 suka mutu a ranar Laraba a lokacin da wani bom ya fashe a ƙauyen Ƴar Tasha.
Haka ma a ranar Lahadi ne bom ya tarwatsa wata mota ƙirar Bus inda direban wanda shi kaɗai ne acikin ta, ya rasa ransa.
