Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Wani marubuci na cewa, kamanni da halayyar marubuci ba su ne abin dubawa ba, yadda ya yi amfani da basirarsa wajen ba da labari ita ce muhimmi.
Na fara haɗuwa da Nafisa Auwal ƙaura Goje ne a wajen wani taron marubuta da aka gudanar a Birnin Kano, lokacin da aka ba ta shaidar nasarar da ta samu ta zama ta ɗaya a gasar rubutun Gajeren Labari wanda Zauren Marubura na manhajar WhatsApp ya shirya.
Ganin nasarar da wannan marubuciya ta samu ya bai wa jama’a da dama mamaki, ba ma ni kaɗai ba, ganin manyan marubuta da dama da suka shiga gasar ba su samu nasara ba, sai wannan ƙaramar yarinyar da ba kowa ne ma zai yi mata tunanin marubuciya ce ba.
Duk da kasancewar ba yarinya ce ƙarama sosai a shekaru ba, don aƙalla ta doshi shekara 27, amma ƙaramin jikinta ya sa wasu ke yi mata kallon yarinya. Amma duk wanda ya kusance ta ko ya yi mu’amala da ita, nan zai fahimci lallai Nafisa ‘yar baiwa ce! Tana da kaifin ƙwaƙwalwa da basirar sarrafa kalma, yadda za ta ratsa zukata, kuma ta daki hankalin mai sauraro ko mai karatu.
Littafin ‘Tauraruwa’ ba shi ne na farko da marubuciyar ta rubuta ba, sai dai shi ne na farko da ta wallafa shi har ya fita a matsayin kammalallen littafi na takarda, da aka buga, kuma ya shiga hannun jama’a. Bayan shi tana da wasu rubutattun labarai gajeru da dogaye da suka haura 12 ban da finafinan Hausa da ta rubuta.
Sai dai abin da ya sa littafin ‘Tauraruwa’ ya fita daban shi ne irin sallon da labarin ke ɗauke da shi, wanda kuma ke cike da darussa masu yawa. Labari ne da ya shafi kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Jamhuriyar Nijar da Najeriya, da yadda jami’an tsaron ƙasashen biyu suke haɗin gwiwa a tsakanin su wajen magance matsalar ‘yanta’adda da suke haifar da ƙalubalen tsaro.
Tauraruwa labarin wata yarinya ce mai suna Zaitun, wacce ta taso da maitar son ta samu shahara, ko’ina a riƙa labarin ɗaukakarta, sunanta ta shiga kafafen watsa labarai da jaridu daban-daban. Ba ta da burin da ya wuce ta yi abin da hankalin kowa zai koma kanta, don haka ne ma ta yi wa kanta laƙabi da Tauraruwa. Sai dai duk da wannan buri nata ba ta iya samun nasara a jarrabawar kammala sakandire ba, ta kuma kasa samun tsayayyen saurayi, saboda yadda take raina duk wanda ya zo neman auren ta, musamman idan ta lura zama da shi ba zai kawo mata ɗaukakar da take nema ba. A dalilin haka ta rabu da samarinta, Sagir da Mustafa da suka nuna suna son ta da gaske, amma ita ta ƙi nuna musu kulawa da soyayyar da suke buƙata daga gareta, saboda hankalinta yana kan harkokin da take yi a zaurukan sada zumunta, a ƙoƙarin ta na neman ɗaukaka da shahara. A irin haka ne ta je ta yi gamo da wani ƙasurgumin ɗanta’adda, wanda jami’an tsaro a Jamhuriyar Nijar ke nema ruwa a jallo, Yuosuf Kasheem. Sakamakon yadda take ganin hoton sa a waya yana yi mata kyau, ta riƙa amfani da wannan hoton da sunan shi ne wanda za ta aura, domin tura wa tsohon saurayinta haushi kan auren da ya yi.
A ƙarshe dai, tauraruwa ta samu shaharar da take nema, sai dai ba ta zo mata da alheri ba, domin kuwa sunanta ya shiga ko’ina ana labarin alaƙar ta da madugun ýanta’adda, Yousuf. Ta ja wa kanta da iyayenta mummunan suna da tsangwama daga jama’ar gari, aka riƙa zarginsu da rashin iya tarbiyya ganin abin da ýar su ta aikata, har ya haifar da asarar rayuka.
Duk da kasancewar daga baya Allah ya wanke sunan Tauraruwa an gane kuskuren da ta yi da rashin wayo da ta nuna, har ma a ƙarshe ta auri babban jami’in tsaron da ya taimaka wajen kuɓutar da ita.
Tauraruwa labari ne da ke nuni akan illar rashin zurfafa buri bisa wata buƙata marar ma’ana, da kuma illar bijirewa biyayyar iyaye kamar yadda Tauraruwa Zaitun ta kasance mai tsananin buri akan ɗaukaka da shahara ba tare da wata manufa mai amfani da ta ke da burin cimmawa da ɗaukakar ba. Sannan ta yi gwagwarmaya da iyayenta a ƙoƙarinsu na saita ta akan daidai tana bijerewa, wanda hakan ne ya kai ta ga faɗawa wahala, sai kuma rashin iya mu’amala da mutane a zaurukan sada zumunta. Yana da kyau mu fahimci cewa, akwai mutane da dama da muke mu’amala da su a zaurukan sada zumunta waɗanda bamu da masaniyar haƙiƙanin su waye su. Wani lokaci akwai mutumin da ko da kuɗi idan ka buƙaci ganinsa a zahiri ya fi ƙarfinka, amma dalilin zaurukan sada zumunta sai ka saba da shi, kamar yadda hakan ya faru da Zaitun, ba ta da masaniyar waye Muƙaddas ban har ta saki baki da maganganun da suka jefa ta matsalar da ta kusan tafiyar da numfashin ta.
Labarin Tauraruwa ya tsaru sosai, kuma an rubuta shi cikin salo mai jan hankali, da riƙe mai karatu. Sannan wani abin burgewa shi ne yadda aka kula da ƙa’idojin rubutu, da tsaftataccen tsarin isar da saƙo, wanda ba ya tare da wasu kalmomi na batsa ko kalaman da ba su dace ba. Littafi ne da kowa zai iya karantawa, manya da yara, don yana ƙunshe da darussa masu muhimmanci. Daga ciki akwai illar bijirewa iyaye, ƙarfafa kishin ƙasa, da kuma nadama bayan kuskure.
Sannan harwayau, a yanayin da ake ciki na taɓarɓarewar tsaro a ƙasar nan, da yadda ‘yanta’adda suke cin karensu babu babbaka, a dazuka da ƙauyukan da ke tsakanin iyakokin Najeriya, suna tserewa daga wannan ƙasa zuwa waccan. Ba da jimawa ba, mun ga yadda haɗin gwiwar jami’an tsaron Najeriya da Nijar suka fatattaki ‘yanta’addan Lakurawa daga maɓoyarsu da ke kan iyakar ƙasashen biyu. Lokaci ya yi da jami’an tsaro ya kamata su ƙarfafa gwiwar marubuta wajen yin rubuce-rubuce da za su ƙara faɗakar da jama’a da wayar musu da kai wajen yin rubuce-rubuce irin wannan. Da haka nake ganin za su taimakawa ƙoƙarin da suke yi, a matsayin su na ‘yan ƙasa nagari.
Abin mamaki shi ne yadda wannan marubuciya mai ƙananan shekaru da wayewa ta iya rubuta wannan hamshaƙin labarin duk da kasancewar ba ta san komai ba a harkar tsaro, kuma ba ta taɓa zuwa Nijar ba, in ka ɗauke zaman maƙotaka ko zumunci na kafar sadarwa da ake yi da wasu.
A cewar marubuciya Nafisa Auwal ƙaura Goje, shekaru biyu ta shafe tana ƙoƙarin rubuta wannan littafi, saboda sarƙaƙiyar da ke cikin labarin, da binciken da ta riƙa yi, kan yadda ayyukan jami’an tsaro yake a irin wannan yanayi da salon da labarin ya ɗauka. Don har Sufeton ýansanda aka haɗa ta da shi wanda ya riƙa taimaka mata da bayanai, da kuma amsoshin tambayoyin da ta riƙa yi masa. Ta fara tunanin rubuta wannan labarin na Tauraruwa ne a lokacin da na saurari wata hira da tashar rediyon BBC ta yi da wata budurwa wacce ta cimma wata nasara a rayuwarta. Ganin yadda abin ya burge ta ne sosai shi ne har ta yanke shawarar rubuta labarin Tauraruwa.
Burin marubuciyar shi ne labarin Tauraruwa ya zamo darasi musamman ga matasa maza da mata. Ga ɓangaren mata zai tsoratar da su daga halayya irin ta Zaitun. Ga samari kuma halayyar Muƙaddas da Sufeta za ta koyar da su yadda ake nuna kishin ƙasa da samar da al’umma tagari.
