“Marubuci tamkar fitila ce da ke haska al’umma”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Nabila Aninu Dikko, marubuciya ce mai nasibi, wacce Allah Ya tarfawa garinta nono, a fagen rubutun adabi. Ta rubuta littattafai 15, kuma har kawo yanzu tana cigaba da rubutu. Marubuciya ce da ta fito daga Jihar Kebbi, kuma take hangen watarana za ta kawo sauyi mai tasiri da zai canza akalar rubutun adabin Hausa a ƙasar nan, idan ta samu damar da take burin samu. A tattaunawar ta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, Nabila ta bayyana cewa, babban jarinta a harkar rubutu shi ne masu karanta littattafanta.
MANHAJA: Ki gabatar mana da kanki.
NABILA DIKKO: Assalamu alaikum wa rahmatullahi ta’ala wa barakatuhu. Da farkon sunana Nabila Aminu Dikko, wacce duniyar marubuta, makaranta har ma da mahukunta suka fi sani da Nabeela Dikko. Ni marubuciya ce, makaranciya, mai nazarin rubuce-rubucen adabi. Allah Ya albarkace ni da yin aure, kuma ina sana’a domin dogaro da kaina.
Ki ba mu tarihin rayuwarki.
An haife ni a shekarar 1994 a ƙaramar Hukumar Argungu da ke Jihar Kebbi. Na fara neman ilimi da karatun Islamiyya, wanda har yanzu muna kan wannan turba. Alhamdulillah, na yi nasarar sauke Alƙur’ani mai girma da littattafan addini. A ɓangaren boko kuma, na fara tun daga matakin firamare, har sakandire zuwa lokacin da na kammala kwalejin ilimi inda na samu shaidar koyarwa ta NCE a 2018, na karanta Hausa/Islam. A yanzu kuma ina fafutukar ƙarawa gaba, in sha Allah.
Ki bamu labarin yadda rayuwa ta kasance miki yayin tasowarki, wacce irin gwagwarmaya aka fuskanta?
Alhamdulillahi, a kullum ina godewa Allah (SWT) da Ya yi ni Musulma jinin Musulmai kuma na fito daga zuriya mai albarka. Na samu ilimi da tarbiyya yadda ya dace. Rayuwata tana cike da abubuwa mabambanta, domin duk wata rayuwa darasi ce. Na taso a wurin kakata, wato mahaifiyar babana kenan. A ganina babu rayuwar da take miƙawa ɗoɗar ba tare da ta fuskanci gwagwarmaya mai daɗi da akasin haka ba. Saboda haka an sha gwagwarmaya a wurin mu’amala da abokan karatu da sauran sabgogin rayuwa ta yau da kullum.
Wanne ƙalubale kika fuskanta da ya koya miki wani muhimmin darasi a rayuwarki?
Babban ƙalubalen da na fuskanta a rayuwa wanda har ya zame mini darasi shi ne kuma yake tuna min da kalmar nan da ake ce wa, ‘Mahaƙurci mawadaci’. Wannan karin maganar ya yi matuƙar tasiri a rayuwata, saboda duk wani abu da zai zame mini ƙalubale da zarar na yi haƙuri na roƙi ubangijina sai na ga abin ya zo ya wuce, har ma ya zame mini alheri. Darussan rayuwa suna da yawa ga duk wani mai cikakken hankali, saboda haka a kullum ina ganin darasi a rayuwata, ko kuma ta wasu, domin duniya makaranta ce, in kuma kana ciki ba zaka rasa ɗaukar darussan rayuwa ba.
Wanne abu ne za ki iya cewa, ya taimaka wajen mayar da ke irin macen da yanzu kika zama?
Addu’ar iyaye da kuma taimakonsu, saboda da ban yi karatu na koyo rubutu ba da ban kawo wannan babban matsayin ba, wanda ba kowa ke samu ba sai wanda ubangiji ya yardar masa. Haka addu’oin su suna taka rawa a rayuwata yadda har na zama nutsattsiya wacce za ta zauna ta yi tunani da nazari, har ma da bincike mai zurfi, don ganin na kawo abin da zai taimaki rayuwar al’umma.
Mene ne ya ja hankalinki kan rubutun adabi?
Babban abin da ya ja hankalina wurin ganin na fara rubutu, shi ne saƙo. Ina so na isar wa ‘yan uwa saƙona ta hanyar rubutu, shi ya sa na ke zaƙulo manyan matsaloli in yi rubutu a kansu, ta yadda al’umma za su karanta su amfana.
Ina son adabi sosai. Ni mai kishin adabin Hausa ce, sannan ba zan gajiya da bayar da gudunmawata ba wurin ganin an inganta adabi da bunƙasar harshen Hausa ba.
Yaushe kika fara tunanin fara rubuta labarin kanki, kuma ko za ki iya tuna yaya labarin yake?
Na fara ƙirƙirar labarina na kaina tun a shekarar 2012, a lokacin ina ajin ƙarshe na sakandire, wato SS 3. Na rubuta labarin a littafi, kuma na gina shi ne akan illar wulaƙanci, girma kai, da gadara. A lokacin da na ba ƙawata don ta karanta sai take ce mini labarin ya yi daɗi sosai. Hakan shi ya ƙarfafa mini gwiwar cigaba da ƙirƙirar labarai, har ya kai ga ina fitar da littafi sukutum!
Kawo yanzu kin rubuta littattafai guda nawa? Kawo sunayensu da bitar uku daga ciki.
Na rubuta littattafai kamar 15 wasu na da kashi 2, wasu kuma iya littafi ɗaya ne.
Daga cikin littattafan da na rubuta akwai,
‘Auren Dole!’ ‘Almajiranci ko Aikatau?’ ‘Baƙar Aƙida’, ‘Bodarar Amarya’, ‘Dangin Miji’, ‘Duk Abin Da Ka Shuka’, ‘Idan An Ciza…, ‘Laifin Waye?’ ‘Mari ɗaya’, ‘Matan Aure’, ‘Sanin Gaibu’, ‘Sirrin Mowa’, ‘Tarbiyya’, ‘Tsantsar So’, ‘ƙwai A Baƙa’, ‘Kowa Ya Ci Bashin Kura’, da kuma ‘Uwar ‘Yan Mata’.
Kamar shi littafin, ‘Uwar ‘Yan Mata’, labari ne da na gina akan jigon illar nuna bambanci a tsakanin jinsi da wasu mutane suke yi. Ya ƙunshi irin ƙalubalen da wasu mata ke fuskanta akan yawan haihuwar ‘ya’ya mata. Sakamakon yadda wasu mazajen suke jahiltar hakan, har ma da nuna tsanar su akan yaran ko kuma uwar da dai sauransu.
Shi kuma littafin, ‘Tarbiyya’ yana ɗauke ne da labarin wani matashin saurayi wanda yake cikin ganiyar kuɗi da iko, ya taso da wasu halaye marasa kyau, saboda irin tarbiyyar da ya taso da ita. Yayin da ya haɗu da tauraruwar labarin, Batool, ita kuma ‘yar talakawa ce. Amma iyayenta sun bata ilimi da tarbiyya mai kyau. Yayin da babin ƙaddarar su ya buɗe lokaci ɗaya sai ƙaddara ta haɗa su, daga nan kuma gwagwarmaya ta soma.
Littafin, ‘Almajiranci Ko Aikatau’, labari ne da na gina akan illar tura yara almajiranci da iyaye ke yi, ba tare da ana bibiyar halin da suke ciki ba, da kuma taimakonsu da abubuwan da za su iya buƙata na yau da kullum. Haka ɓangaren mata su ma ana tura su birni wurin aikatau ba tare da an yi la’akari da tarbiyyar gidan da za a tura ta ba da dai sauransu.
Wanne littafin ne ya fara ɗaga sunanki a tsakanin marubuta?
A duk lokacin da na ɗaura alƙalamina na fara rubutu to, gaskiya ina samun saƙonni daga ‘yan uwa marubuta. Amma littattafan, Tarbiyya, Uwar ‘Yan Mata, da Bodarar Amarya, masu karatu da dama sun bibiye su, a lokacin da nake rubuta su.
Yaya alaƙarki da masu karatun littattafanki, ta yaya kike mu’amala da su?
Da akwai kyakkyawar alaƙa a tsakanina da sanyin idaniya ta, wato makaranta, saboda su ne ƙashin bayan duk wata nasarata, ina sauraren su sosai, ina mu’amala da su tamkar ‘ýan’uwana, duk wanda ya zo da buƙatarsa ina dubawa daidai gwargwadon hali.
Wanne abin farinciki ko akasin haka ne ya taɓa faruwa da ke ta sanadiyyar rubutu wanda ba za ki manta da su ba?
Abin farincikin da ya faru da ni sanadin rubutu, suna da yawa. Kaɗan daga ciki su ne haɗuwa da ‘yan’uwa marubuta masu zuciyar zinare. Ni da su mun zama tamkar jini ɗaya, duk da muna mabambantan wurare. Hakan bai hana mu ɗaukar junan mu tamkar muna kusa ba. Sanadin rubutu na haɗu da mutane masu daraja sosai. Sannan harwayau, na samu nasara ta fannin gayyata da samun damar halartar zuwa hira a gidajen jaridu, kamar rediyon Eƙuity FM Birnin Kebbi, inda har sun karanta littattafaina. Na samu arziƙin samun mutane da yawa a rayuwata, wanda suke yi mini addu’a kan abubuwa da dama. Alhamdulillah.
Ta yaya ki ke samun jigon da ki ke rubutu a kai?
A yanzu nan da muke hirar nan ma zan iya samun jigo, saboda haka jigo ba ya yi mini wahalar samu, a gida ko waje, duk inda na tsinci kaina zan iya samun jigon da zan gina labari.
Wanne salon rubutu ne ya fi baki sha’awa, almara, yaƙe-yaƙe, sarauta, ko soyayya?
Kowanne salo yana burgeni kuma zan iya yin rubutu a kai, in sha Allah.
Wanne labari ne ya fi baki wahalar rubutawa ko ki ka fi jin sauƙin rubutunsa?
Duk labarin da za a ƙirkira a ganina yana da wahala, saboda sai an zauna an yi tunani, an kuma yi bincike, tare da neman sanin abin da ba a sani ba a wurin masana. Rubutu ba abin da za a zauna a rubuta kara-tsaye ba ne, domin shi marubuci tamkar fitila ce da ke haskawa al’umma daidai da kuma akasin hakan. A ganina wajibi ne a inganta hasken wannan fitilar, kar a je gyaran ɗaya goma ta zo ta lalace.
Wane ne ya fi taimaka miki wajen sanin ƙa’idojin rubutu, don inganta labarinki?
Aƙwai mutane da dama da suke taimaka min wajen ɗora ni akan hanya yadda zan inganta rubutuna. Daga ciki akwai, Marigayi Zainuddeen Jibril, Allah Ya jiƙansa da rahama. Sannan akwai Malam Jibril Adamu Rano, da kuma Malam Yusuf Yahaya Gumel.
Wacce ƙungiyar marubuta ki ke, kuma wacce gudunmawa take baki ga cigaban rubutunki?
Adabi Writers Association ita ce ƙungiyata, kuma tana bani taimako ta kowacce fuska, domin inganta rubutuna da na sauran ‘ya’yan ƙungiya.
Kin taɓa shiga wata gasar marubuta, wanne sakamako ki ka samu?
Ina shiga gasanni sosai, amma labarina yawanci ya fi fitowa ne a matakin farko, ban cika tsallake matakin ƙarshe ba. Amma na yi nasara a Gasar Gwarazan Hikayata na 2022, wanda har suka ɗauki nauyin buga littafina ‘Uwar ‘Yan Mata’.
Wanne abu ne kike ganin idan kin samu dama za ki iya yi don kawo canji a harkar rubutun adabi?
A duk lokacin da dama ta bani damar damawa, zan kawo damar da marubuta za su dama a harkar rubutu, zan ciyar zan kuma shayar da adabi, zan kawo sauye-sauyen da za su inganta shi. Abin da zan canja shi ne rubutun batsa, wanda wasu suke kira da Adabin Bariki, wannan zai zama tarihi, in sha Allah.
Wane ne madubin kwaikwayonki a cikin marubuta, maza ko mata?
Allon ƙwaiƙwayona a maza shi ne Malam Jibril Adamu Rano, a mata kuma Fauziyya D. Sulaiman.
Mene ne babban burinki nan gaba a harkar rubutu?
Babban burina shi ne littattafaina su zaga ko’ina a duniya, har in samu waɗanda za su daki ƙirji su buga. Misali, ina son rubutuna ya zama allon ƙwaiƙwayon wasu.
Wanne karin magana ne ke tasiri a rayuwarki?
Mahaƙurci Mawadaci.
