2027: Za mu yi aiki tuƙuru don rage tasirin Jam’iyyar APC a Kano – Kwankwaso

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya sha alwashin yanke ƙuri’un jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) a zaɓen 2027, da nufin rage goyon bayan jam’iyyar zuwa ƙuri’u 15,000 kacal a jihar.

Kwankwaso ya yi wannan alƙawarin ne a wata ganawa da ya yi da tsofaffin kansiloli da kuma manyan mashawarta na musamman da suka yi aiki a tsohuwar gwamnatinsa, tare da masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumar Tsanyawa, a gidansa da ke Kano.

Da yake waiwayen zaɓukan 2023, Kwankwaso ya yaba da ƙwazon da tawagarsa ta yi wajen samun gagarumin sakamako.

Duk da cewa jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ta kasance sabuwar jam’iyyar siyasa da kuma ƙaddamar da yaƙin neman zaɓenta a makare, jam’iyyar ta ɗauki hankali sosai, inda jam’iyyar PDP ta samu ƙuri’u 15,000 a Kano.

“Yanzu, lokaci ne na mu don rage tasirin APC. Za mu yi aiki tuƙuru don ganin an rage musu ƙuri’u zuwa ƙasa da 15,000 a Kano zuwa 2027,” inji Kwankwaso.

A yanzu dai ya mayar da hankali kan zaɓen 2027, Kwankwaso ya bayyana aniyarsa ta rage tasirin jam’iyyar APC a jihar, inda ya jaddada buƙatar yin namijin ƙoƙari da haɗa kai don ganin jam’iyyarsa ta samu rinjaye.

Ya kuma buƙaci magoya bayansa da su jajirce da kuma yin aiki tuƙuru domin ganin an samu gagarumar nasara a zaɓe mai zuwa.

By ukarofi