Faretin ban girma da aka yi wa Seyi Tinubu bai kamata ba, inji Atiku

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi Alla-wadai da faretin ban girma da ka yi wa ɗan gidan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu, yana mai bayyana hakan a matsayin saɓa wa al’ada rundunar sojin Nijeriya tare da nuna buƙatar a gudanar da bincike kan al’amarin.

A cikin wata sanarwa da ofishin mai magana da yawun Atiku ya sanya wa hannu, Paul Ibe, Atiku ya nuna rashin jin daɗinsa game da yadda aka saɓa wa dokar rundunar sojin Nijeriya na haɗa faretin girmamawa ga shugabannin.

Atiku ya ƙalubalanci sahihancin sashen rundunar sojin da ake kira da “Nigeria Cadet Network,”. Ya kuma jaddada cewa amfani da sunan abu ne da zai tauye darajar rundunar sojin Nijeriya.

“A ƙoƙarin gano gaskiyar abin kunya da ya faru na faretin girmamawa, mun kafa kwamitin masana shari’a da sha’anin tsaro domin bincike kan sahihancin ‘Nigeria Cadet Network.’ ga mamakinmu wannan ƙungiya ba ta da rajista a hukumance kuma abin damuwa shi ne, amfani da bindigu da fararen hular suka yi a yayin faretin a lokacin da ake fama da fargabar bazuwar haramtattun makamai a faɗin ƙasar nan,” in ji Atiku.

Daga nan ne ya buƙaci a hukumomin tsaro da su gudanar da bincike kan waɗannan muhimman abubuwa:

Duba sahihancin ƙungiyar “Nigeria Cadet Network” da amfani kalmar “Cadet” bayan ba ta da rajista.

Asali da sahihancin makaman da suke riƙe da su a hukumance.

Duba dacewar faretin girmamawar da rundunar ta yi wa ɗan shugaban ƙasar nan da sunan jami’an tsaro.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma jaddada muhimmancin kare martabar rundunar sojin Nijeriya a matsayin abu mai muhimmanci.

“Idan ta tabbata cewa ɗan shugaban ƙasar da waccen ƙungiya sun aikata wani abu da ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Nijeriya, ya kamata a ɗauki mataki na shari’a a kansu da waɗanda suke da hannu a ciki,” inji Atiku.

By ukarofi