Daga USMAN KAROFI
Ƙasashen Nijar, Mali da Burkina Faso da ke ƙarƙashin mulkin soja sun bayyana ficewarsu daga ƙungiyar (ECOWAS). Ƙungiyar ta ECOWAS ta sanar da wannan mataki a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, 29 ga Janairu, 2025, wanda ya kawo ƙarshen ƙoƙarin da Ƙungiyar ke yi na shawo kan ƙasashen su ci gaba da kasancewa a cikinta.
Duk da ficewar ƙasashen, ECOWAS ta bayyana cewa a cikin ruhin haɗin kai da moriyar al’ummomin yankin, za ta ci gaba da ba da dama ga ‘yan ƙasashen guda uku su yi amfani da fasfo da katin shaidar da ke ɗauke da tambarin ECOWAS. Haka nan, ƙasashen mambobin ECOWAS sun amince da ci gaba da karɓar kayayyaki da hidimomi daga waɗannan ƙasashe bisa tsarin yarjejeniyar cinikayya ta ECOWAS (ETLS).
Haka kuma, Ƙungiyar ta ce ‘yan ƙasashen uku za su ci gaba da amfana da ‘yancin zirga-zirga, zama, da kafa kasuwanci ba tare da an buƙaci biza ba, kamar yadda yarjejeniyoyin ECOWAS suka tanada, har zuwa wani lokaci da za a yanke shawara kan tsarin sabuwar hulɗa da su. Har ila yau, ECOWAS ta buƙaci a ci gaba da bai wa jami’anta da ke aiki a cikin ƙasashen uku goyon baya da cikakken haɗin kai.
ECOWAS ta bayyana cewa waɗannan matakai sun zama dole domin gujewa ruɗani da cikas a rayuwa da kasuwancin al’ummomin yankin yayin wannan matsin lamba na sauyin yanayi. Don haka, ta kafa wani kwamiti da zai tattauna da kowanne daga cikin ƙasashen uku domin fitar da tsarin hulɗar gaba.
