Raɗɗa ya bada umarnin kai jami’an tsaro manyan asibitoci Jihar Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa ya bada umarnin kai jami’an tsaro a manyan asibitoci da ke faɗin jihar musamman a ƙananan hukumomin da ke fama da matsalar tsaro.

Kwamishinan lafiya Musa Adamu Funtua ya faɗa wa manema labarai
haka a ofishin sa,yace gwamnan ya ɗauki wannan mataki ne bayan taron gaggawa na majalisar tsaro a jihar.

Ƙungiyar jinya da unguwarzoma ta ƙasa reshen jihar Katsina tayi barazana na shiga yajin aiki a ƙarƙashin wannan wata idan gwamnati bata samar da cikakken tsaro a asibitoci da ke jihar ba.

A hira da manema labarai, shugaban ƙungiyar Nura mu’azu ya ce kungiyar ta ɗauki wannan mataki ne ganin a kwanakin nan ƴan bindiga ke kai ma jami’an su hare hare a wasu asibitocin jihar.

Ya bada misalin babban asibitin ƙanƙara inda aka sace jami’an su da har yanzu babu labarin wasu a ciki.

Wasu daga cikin buƙatun ƙungiyar sun haɗa da biyan diyya ga ya’yan ƙungiyar da suka rasa rayukansu suna bakin aiki.

Haka kuma ƙungiyar na buƙatar gwamnati ta ƙara kyautata wa jami’an kiwon lafiya ta yadda malaman kiwon lafiya da ke aiki a wasu wurare zasu ji sha’awar aiki a gwamnatin jihar.

Sai kwamishinan lafiya Adamu Funtua ya ce ya zuwa yanzu gwamnatin jihar Katsina ta biya kaso 80% na buƙatar ƙungiyar.

“Nayi magana da babban manajan babban asibitin ƙanƙara ya shaida mani ya fara ganin ƙarin jami’an tsaro a asibitin”inji kwamishinan.

Kwamishinan ya bayyana cewa matsalar da aka samu na rashin sadarwa ne a tsakanin gwamnati da ƙungiyar amma a cewar sa yanzu komai ya daidaita.

By ukarofi