Ƙarancin kayan aiki: Ƙungiyar mafarauta ta nemi agajin gwamnati a Jigawa

Spread the love

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

Gwamnatin Jihar jigawa za ta yi amfani da mafarauta wajen gadin asibitoci, makarantu da sauran ma’aikatun gwamnati a ƙoƙarinta na ganin ta inganta tsaro a dukkan sassan jihar.

Shugaban Hukumar tsaro ta mafarauta da akafi sani da ‘Nigeria Hunters and forest Security Service’, Alhaji sale Umar ya bayyana hakan a wata hira da wakilinmu a jiya Alhamis, a ofishinsa bayan kammala taron mafarauta a ofishinsu dake Fadar Gwamnatin Jihar a Dutse.

Alh sale Umar ya ce tuni yarjejeniya ta yi nisa tsakaninsu da gwamnatin Jihar akan gadin wasu asibitoci da aka ware masu a wasu shiyoyin jihar waɗanda suka haɗa da Asibitin Buji a ƙaramar Hukumar Buji da Asibitin Miga a karamar Hukumar Mai Gatari.

A shiyyar Hadejia wato jigawa ta Gabas aka Basu hakkin Kula da Asibitin Kirikasamma a ƙaramar Hukumar Kirikasamma da kuma Asibitin Kaugama a ƙaramar hukumar Kaugama.

Haka kuma a shiyyar Jigawa ta Arewa maso Yamma aka ba su ikon kula da asibitin Gagarawa a ƙaramar Hukumar Gagarawa da asibitin Ƴankwashi a ƙaramar hukumar Ƴankwashi.

Ya kara da cewa suna da wadatatttun ma’aikata a jigawa da za su yi aikin tsaro tare da yin faɗa da marasa gaskiya matukar gwamnati za ta ba su haɗin kan da suke buƙata.

Ya kuma buƙaci gwamnati ta taimaka masu wajen biyan ma’aikatansu alawus-alawus kasancewar su a matakin sa kai suke ganin cewa gwamnatin tarayya ba ta fara biyansu albashi ba.

By Babaji