Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Mai martaba Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sanar da soke duk wasu shirye-shiryen gudanar da bukukuwan Sallah ƙarama a faɗin Jihar Kano.
Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne a cikin wani ɗan taƙaitaccen faifan bidiyo a daren Larabar nan, inda ya bayyana dalilan da suka sa aka dakatar da shirin hawan.
Idan dai za a iya tunawa, Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya sanar da jami’an tsaro musamman rundunar yan sanda ta ƙasa shirinsa na gudanar da bukukuwan Sallah.
Idan kuma za’a iya tunawa, Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya umarci mai martaba Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II tare da sarakuna masu daraja ta biyu da su shirya don gudanar da bukukuwan Sallah ƙarama a faɗin jihar Kano baki ɗaya domin tunawa da shagalin sallah.
Hakan dai ya haifar da razani da zaman ɗar-ɗar da kuma tunanin abinda kaje ya zo, lamarin da ya sa ƴan sanda suka baiwa jama’a tabbacin kare rayuka da dukiyoyin su kafin da kuma bayan bukukuwan ƙaramar Sallah.
Kazalika, Aminu Ado ya bayyana a cikin faifan bidiyon cewa ya soke bikin ne saboda ƙoƙarin da wasu malaman addinin musulunci masu daraja da kuma dattawa suka yi wajen ganin an samu zaman lafiya.
“Dole ne mu dakatar da shirin gudanar da wannan al’amari sakamakon shawarwari da malaman addinin Musulunci masu daraja da kuma dattawa suka bamu,” inji Aminu Bayero.
