UTME 2025: JAMB ta kama mutum 40 da ke da alaƙa da satar amsa a jarrabawar

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a ta ƙasa (JAMB) ta ce ta gano mutum sama da 40 da suke da akaƙa da laifin satar amsa a jarrabawar bana.

Rajistaran JAMB Is-haƙ Oloyede ya sanar da haka wa manema labarai a hedikwatan hukumar ranar Litinin.

Oloyede ya ce mutanen na tsare a hannun jami’an tsaro inda da zaran an kammala bincike za a yanke musu hukunci bisa ga laifin da suka aikata.

Ya ce hukumar ta ɗauki wasu tsauraran matakan samar da tsaro domin kawar da matsalar satar amsa a jarabawar wanda suke aiki yayin da ɗalibai ke rajistan jarrabawar, kafin ɗalibai su shiga wurin rubuta jarrabawar da yayin da ɗaliban ke rubuta jarrabawar.

Idan ba a manta ba a shekarar da ya gabata hukumar jarrabawar ta sanar cewa ɗalibai sama da miliyan 1.9 ne suka rajistan jarrabawar inda a bana ɗalibai sama da miliyan biyu.

A shekarar bara hukumar ta ƙwace sakamakon jarrabawar ɗalibai 64,000 bisa zargin satar amsa inda bayan ta kammala gudanar da binciken ta saki wasu sakamakon bayan ta tabbatar ba su da alaƙa da satar amsa.

By ukarofi