Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, da kuma tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi, a birnin Rome na ƙasar Italiya. Taron ya faru ne a yayin bikin ƙaddamar da sabon Fafaroma, Leo XIV, a Vatican City. A cewar mai magana da yawun Tinubu, Bayo Onanuga, Fayemi ne ya lura da Tinubu yana zaune tare da wasu shugabanni, sai ya roƙi Obi da su je su gaishe da shi. Obi kuwa ya amince.
A lokacin da suka isa wajen shugaban, Fayemi ya fara da cewa: “Shugaban ƙasa, barka da zuwa cocinmu, muna godiya da halartar bikin Fafaroma.” Tinubu ya amsa da dariya yana cewa: “Ya kamata ni ne zan tarbe ku da Peter. Ni ne shugaban tawagar Najeriya.” Wannan ya sanya Peter Obi dariya, inda ya ce: “Eh, haƙiƙa. Mu mambobin tawagarka ne.”
Peter Obi da Fayemi duka mambobin cocin Katolika ne masu matsayi na Papal Knights. A lokacin bikin, Shugaba Tinubu ya yi musabaha da sabon Fafaroma Leo XIV, tare da wasu shugabanni na duniya kamar Mataimakin Shugaban Amurka J.D Vance da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky. A jawabinsa, Fafaroma ya yi kira da a daina take haƙƙin matalauta da lalata muhalli, yana mai buƙatar cocin ta zama mai kawo sauyi a duniya mai cike da ƙiyayya da rarrabuwar kawuna.
