Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mataimakin gwamnan kuma Amirul Hajji na bana Malam Farouk Lawal Joɓe ya sanar da haka lokacin da ya wakilci gwamna wajen ban kwana da Maniyatan farko da za su tashi zuwa ƙasar Saudiyya.
Ya ce gwamnatin tarayya ta ware kujera na aikin hajjin bana guda 3000 da ɗori amma saboda yanayin tattalin arzikin ƙasa yasa mutane 2047 suka sami biya.
Joɓe ya hori Maniyatan da su zama jakadu nagari tun a nan Katsina har zuwa ƙasa mai tsarki.
Ya gargaɗe su da su guji duk wani abinda zai zubar da mutuncin Nijeriya.
Muƙaddashin gwamnan ya faɗa wa Maniyatan cewa jami’an 175 da suka haɗa da likitoci,malamai masu wa’azi da ma’aikatan hukumar alhazzai na jihar ne za su kasance ko da yaushe suna tare da Maniyatan domin taimaka masu wajen gudanar da ibadar su.
Ya kuma shawarci Maniyatan da su bi a hankali wajen yadda za su kashe kuɗin guzirin su domin kada su sami matsala a can ƙasa mai tsarki .
A nasa jawabin babban daraktan hukumar alhazzai na jihar Hon Yunusa Dankama yayi wa muƙaddashin gwamnan cikakken bayani irin shirin da hukumar ta yi na ganin an gudanar da aikin hajjin bana ba tare da wani matsala ba .
Ya godewa gwamnatin Dikko Raɗɗa bisa irin gudunmawar da ta baiwa hukumar wajen gudanar da aikace aikace na hukumar na yau da kullum.
