Allah ya yi wa Haruna Dauda Biu na VOA rasuwa

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMIN Maiduguri

Allah ya yiwa wakilin gidan rediyon Muryar Amurka (VOA) a jihohin Borno da Yobe, Haruna Dauda Biu rasuwa, da yammacin ranar yau Lahadi a birnin Maiduguri ta jihar Borno.

Malam Haruna Dauda, kuma tsohon shugaban ƙungiyar kafafe yaɗa labaru daban-daban dake aiki a jihar Borno (Correspondents Chapel).

Marigayin, ya rasu ne bayan doguwar jinya da ya sha fama da ita, kuma an tsara gudanar sallar jana’izarsa gobe Litinin idan Allah ya kaimu, a kofar gidansa dake STATE LOW-COST a Maiduguri.

Tuni dai yan uwa da abokanan aiki suka bayyana kaɗuwa tare da bayyana alhinin rashin abokin aiki, dattijo mai halin dattaku. Yayin da suka yi addu’ar Allah ya jiƙanshi da rahama kuma ya sa aljannatul Firdausi ce makomarsa, ameen.

By ukarofi