2027: Ku shirya bankwana da kujerunku – Gwamnan Jigawa ga ƴan majalisa na PDP

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya yi kira ga mambobin Jam’iyyar PDP da ke Majalisar Dokoki ta Ƙasa da su shirya sauka daga mukamansu a babban zaben shekarar 2027.

Ya faɗi hakan ne a yayin taron shirin damawa da al’umma na ‘Citizens Engagement Programme’ da aka yi wa laķabi da ‘Gwamnati da Jama’a’ a Dutse, Babban Birnin jihar.

Haka kuma a taron ne kimanin mambobin Jam’iyyun PDP da NNPP guda 3,502 ne suka sauya sheka zuwa Jam’iyya mai mulki, APC.

Ya yi ikirarin cewa, APC za ta sake nasar a dukkan kujerun da bangaren adawa ke riƙe da su da suka samu a zaben 2023.

Gwamna Namadi ya ce APC tana ƙara samun karbuwa a Kudu maso yammacin jihar a sakamakon ƙoƙarinsu na inganta al’umma da samar da ci-gaba a yankin.

A yayin zaben 2023 ne PDP ta samu nasara a manyan muķamai na majalisa wanda daga ciki akwai kujerar sanatan yankin Jigawa ta Kudu maso Yamma, kujerar ƴan majalisar wakilai a mazabun Birnin Kudu/Buji da Dutse/Kiyawa da kuma kujera a majalisar dokokin jihar.

Kazalika, ya jaddada aniyar gwmanatinsa ta cigaba da yi wa al’umma hidima a karkashin jagorancin APC.

By Babaji