Gwamnati ta fara biyan tsofaffin ƴan hidimar ƙasa ragowar alawus ɗinsu na N44,000

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnatin Tarayya ta fara biyan ragowar alawus ɗin N44,000 na mafi ƙarancin albashi ga tsofaffin ƴan hidimar ƙasa NYSC.

Hakan cika alķawari ne da gwamnatin ta yi, wanda ya dace da sabon tsarin mafi ƙarancin albashi, lamarin da ya haura da alawus ɗinsu daga N33,000 zuwa N77,000.

Ana biyan kuɗin ne kaɗai ga waɗanda suka kammala hidimarsu gabannin fara aiwatar da biya da sabon tsarin albashi.

Tuni dai wasu daga cikin tsoffin ƴan hidimar suka fara tabbatar da samun ragowar kuɗaɗen nasu a asusun bankunansu ta kafafen sada zumunta musamman ta kafar X.

Da dama daga cikinsu sun yaba wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tare da nuna farin cikinsu akan ci-gaban.

By Babaji