Rikicin Gaza na ƙara tsananta: Asibitoci sun cika da gawawwaki

Spread the love

A cikin yanayin da ke ƙara taɓarɓarewa a Zirin Gaza, hukumar Red Cross ta bayyana cewa, asibitocin yankin sun cika da gawawwaki da jikkatatu sakamakon hare-haren da ake kai wa wuraren rabon agaji, lamarin da ya haddasa mafi yawan asarar rayuka da aka taɓa gani tun daga ɓarkewar rikicin.

“Adadin jikkatatu da mamata na da yawa fiye da duk abin da muka fuskanta a shekara ɗaya da ta gabata gaba ɗaya,” inji Red Cross.

Tun daga ƙarshen watan Mayu, asibitin filin Red Cross da ke Gaza ta Kudu ya ruwaito mutuwar mutane 200 da kuma jikkatatu fiye da 2,200, mafi yawansu maza da samari da ke neman abinci da taimako ga iyalansu.

A cikin irin wannan yanayi, ma’aikatan lafiya sun haɗa gwiwa da wasu ɓangarori domin ceto rayuka. Likitocin jinya na taimaka wa wajen duba raunuka, masu tsabtace asibiti sun koma jigilar marasa lafiya, kuma ma’aikatan haihuwa sun shiga aikin kula da masu shan wahala.

Dakta Sally, jami’ar kula da lafiyar kwakwalwa da ta fi mai da hankali kan yara, ta bayyana wani misali mai sosa rai:

 “Wani yaro ɗan shekara shida ya rasa mahaifinsa, mahaifiyarsa da ‘yar uwarsa. Ya kasance cikin mawuyacin hali na gaskiya tsawon makonni uku. Har sai da muka ƙara masa jini ta kwakwalwa kafin ya fara karɓar gaskiyar da ta faru.”

Hukumomi sun tabbatar da cewa, sojojin Isra’ila sun faɗaɗa farmaki, ciki har da kwace yankunan da ke cike da mafakar ‘yan gudun hijira, ciki har da al-Bureij Camp, inda aka kai hari kan wata makaranta da ke da ‘yan gudun hijira ciki. Hotuna sun nuna yara na tsaye cikin hayaƙi, da ke rike da kayan wasan yara a hannunsu, da fuska cike da shakku da tsoro.

“Waɗannan hare-hare ba su da wani dalili sai wargaza iyali da sanya fargaba da tsoro a zuciya,” inji wani mazaunin yankin da ya rasa ‘ya’yansa biyu.

A gefe guda, ana ci gaba da tattaunawar tsagaita wuta a birnin Doha na ƙatar tsakanin Hamas da Isra’ila. Tattaunawar wadda ake gudanarwa ta hanyar wakilai ba kai tsaye ba ta fi mai da hankali kan:

Sakin waɗanda aka yo garkuwa da su a matakai daban-daban, janyewar dakarun Isra’ila daga sassan Gaza, da kuma shigar taimakon jin ƙai cikin walwala.

Sai dai har yanzu Isra’ila ta nace cewa ba za ta dakatar da faɗa ba sai an saki dukka ‘yan ƙasarta da aka yi garkuwa da su, da kuma buƙatar rushe Hamas, yayin da Hamas ke cewa sai an dakatar da yaƙi kafin a yarda da sakin fursuna. Wani minista a gwamnatin Netanyahu, Zeeɓ Elkin, ya bayyana cewa akwai “gagarumar dama” a samun tsagaita wuta, sai dai akwai “batutuwan da ke buƙatar gyara”.

A wani matakin siyasa, shugaban ƙasar Kolombiya, Gustaɓo Petro, ya soki Isra’ila da ƙasashen da ke “yin shiru” yayin da ake kisan ƙilla. A cikin wani sharhi da jaridar The Guardian ta wallafa, ya ce: “Idan muka kasa ɗaukar mataki yanzu, mun zamo abokan laifin abinda gwamnatin Netanyahu ke aikatawa.”

Kolombiya ta dakatar da fitar da kwal zuwa Isra’ila, a matsayin martani ga matakin. Haka kuma ƙasashen Afirka ta Kudu da Malaysia sun ɗauki matakan hukuma, kamar kai Isra’ila gaban kotun duniya da hana jiragen ruwa masu tutar Isra’ila sauka a gaɓar tekunsu.

By ukarofi