Ambaliya ta hallaka fiye da 100, yayin da dubban gidaje suka nutse a Texas

Spread the love

Wata mummunar ambaliya da ta shafi yankin Kudu da Tsakiyar Jihar Texas, daga ranar 4 zuwa 7 ga Yuli, ta haifar da bala’i mafi muni da aka shaida a cikin shekaru da dama, inda aka tabbatar da mutuwar mutane 118 yayin da fiye da 180 suka ɓace.

Lamarin ya tsananta a cikin ƙanƙanin lokaci, yayin da ruwan sama mai nauyi cikin sauri ya haddasa cika gari da ruwa da wuce gona da iri. Ambaliyar ta kwashe gidaje, makarantu, cibiyoyin lafiya da ababen more rayuwa a cikin hanzari, abin da ya bar dubban mutane cikin halin tsaka mai wuya da rashin mafaka.

Rahotanni sun bayyana cewa, tsarin gargaɗin hadari na sirena ya kasa isar da saƙon gaggawa a kan lokaci. Wannan ya sanya mutane da dama suka maƙale ba tare da sanin matsalar da ke tafe ba, lamarin da ya ƙara tsananta adadin mutuwa da ɓacewa.

A wani ɓangare mai tada hankali, an ruwaito cewa, yara mata guda 27 daga sansanin kwana na Camp Mystic sun hallaka sakamakon ɓarkewar ruwan, kuma har yanzu ba a gano gawarsu ba.

Gwamnatin Jihar Texas ta ce, ana ci gaba da aikin ceto domin gano waɗanda suka ɓace, yayin da fiye da mutane 160 har yanzu ba a samu labarinsu ba. ƙungiyoyin agaji da jami’an ceto sun bazama da jiragen sama da na ruwa domin ci gaba da farautar masu yiwuwar rayuwa a ƙarƙashin kango da ruwa.

Haka kuma, an fara bincike kan gazawar tsarin gargaɗi, inda wasu ke zargin akwai kura-kurai a tanadin rigakafin bala’i, musamman duba da irin matsin ruwan da aka rigaya ake hasashen zai sauka.

By ukarofi