Tsaro: Wararrun ‘yan majalisar dokoki a Zamfara sun zargi Gwamna Dauda da yin watsi da al’ummarsa

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Wararrun ‘yan majalisar dokokin Jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Rt. Hon. Bashir Aliyu Gummi sunyi Allah-wadai da Gwamna Dauda Lawal kan yadda ya yi watsi da jama’arsa a sakamakon taɓarɓarewar tsaro a jihar.

Kakakin majalisar wanda ya bayyana hakan a wani zama da sukayi jiya, ya bayyana gwamnatin jihar a matsayin rashin nuna tausayi, rashin sanin yakamata da rashin mutuntawa da irin yadda gwamnatin Dauda Lawal tayi watsi da mutanen jihar waɗanda a hannun ‘yan ta’adda suka addaba.

Ya koka da yadda al’ummar da ba suji ba su gani ba ta’addanci a cikin mako guda ciki har da yankin Jangebe da ke Talata-Mafara inda aka yi garkuwa da ɗaruruwan mutane tare da kashe wasu a yankin Damri da ke ƙaramar hukumar Bakura da Kyambarawa a ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda da kuma Mada a ƙaramar hukumar Gusau.

“Gwamnan bai ma jajanta wa waɗanda abin ya shafa ba ballantana ya aika da wani tallafi ga iyalan waɗanda abin ya shafa amma ya fice ya ci gaba da hutunsa na shekara ba tare da nuna damuwa ko tausaya wa waɗanda suka zaɓe mu ba.”

A nasu gudunmuwar mabanbantan yankin Bakura da Bukkuyum ta Arewa da Mafara ta Kudu da Tsafe ta Yamma da Bungudu da kuma Ƙaura Namoda ta Kudu, sun ce al’ummar mazaɓar su na fama da matsalar taɓarɓarewar tsaro, don haka gwamnati ba ta da muhimmanci kan tsaron rayuka da dukiyoyin al’ummar da suka zaɓe ta.

Sun kuma kafa kwamiti ƙarƙashin jagorancin Hon. Aliyu Ango Kagara wanda ke da alhakin bincikar yadda gwamnatin jihar ta yi amfani da kuɗaɗen tallafi na kungiyoyin ƙasashen waje.

Hakazalika an wajabta wa kwamitin binciken da su tuntuɓi ofishin ƙasa da ƙasa na dukkan hukumomin bayar da tallafi guda uku na Agile, CSDA, da Acreasal da ke Abuja don sanin jimillar kuɗaɗen da Zamfara ta samu da kuma yadda aka yi amfani dasu a jihar.

By ukarofi