Ministan Jinƙai, Yiltwatda ya zama sabon shugaban APC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Jam’iyyar APC ta shirya sanar da Ministan Jinƙai, Farfesa Nentawe Goshwe Yiltwatda a matsayin sabon shugabanta biyo amincewa da shi da gwamnoni da shugabannin jam’iyyar a mataki na jihohi suka yi.

Hakan na zuwa ne bayan gudanar da zama da yin shawarwari da masu-ruwa-da-tsaki a safiyar ranar Alhamis.

A gudanar da zaman ne ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, wanda shi ne shugaban ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar.

Baki ɗaya gwamnonin sun halarci taron face, na Legas da Akwa-Ibom, waɗanda suka samu wakilcin mataimakansu.

Tun a ranar Laraba ne gwamnonin suka je Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja domin bai wa Shugaba Bola Tinubu ba’asi game da matsayar da suka cimma.

Farfesa Yiltwatda, wanda ɗan Jihar Filato ne, ya samu goyon bayan Shugaba Tinubu a wani yunƙuri na samar da daidaiton addinai a jam’iyyar da kuma Gwamnatin Tarayya.

By Babaji