Mun tafka asarar biliyan N92 na kuɗaɗen waje a 2024, inji BUA

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Kamfanin Siminti na BUA, Abdul Samad Rabiu a ranar Litinin ya bayyana cewa kamfanin ya yi asarar kuɗaɗen waje na Naira Biliyan 92 a shekarar 2024.

Shugaban kamfanin simintin na BUA, wanda ya bayyana haka a taron shekara-shekara na kamfanin a Abuja, ya bayyana cewa an afka asarar ne sakamakon faɗuwar darajar Naira. Rabiu, ya ce an samu sauƙin lamarin sosai a bana. A cewar BUA, a cikin 2023, kamfanin ya yi asarar kuɗaɗen waje na Naira Biliyan 63.

AbdulSamad Rabiu ya danganta hauhawar farashin kayayyaki da matsalolin tattalin arzikin duniya, sai dai ya nuna fatan cewa abubuwa za su kyautatu nan gaba.

“Yanzu haka canjin Dala ya kusa dawowa N1,500. Amma ina da kwarin gwiwa cewa nan gaba kaɗan darajar Naira za ta dawo N1,200 ko kasa da haka. 

“Idan hakan ta faru, farashin kayayyaki zai sauka, ba siminti kadai ba, har da sauran kayayyaki,” inji AbdulSamad Rabiu.

Da yake amsa tambaya kan dalilin da ya sa buhun siminti ya kai kimanin N10,000, Rabiu ya ce hakan ya faru ne saboda tsadar samar da shi, ba wai don neman riba mai yawa ba.

“Tsadar kayan samar da siminti ce ta sa farashin ya kai kusan N10,000. Mun zuba biliyoyin Dala a kamfanin siminti a tsawon shekaru 20 zuwa 30.

“Samun ribar Naira Biliyan N69 bayan haraji, wanda yayi daidai da kusan Dala miliyan 40, akan irin wannan jari ba wani abu ne mai yawa ba.”

Abdul Samad Rabiu ya jaddada cewa farashin makamashi shi ne babban abu da ke haifar da tsada a kamfanin siminti, hakan ya sa suka zuba jari don gina ƙaramin wajen samar da iskar gas.

“Muna kashe kuɗi sosai a ɓangaren gas. Mu na son sarrafa hakan a cikin gida idan zai yiwu,” inji shi.

Duk da ƙalubalen tattalin arziki, ciki har da faɗuwar Darajar Naira da tsadar kayayyakin da ake buƙata, kamfanin simintin BUA ya samu kyakkyawan sakamako a 2024.

Kamfanin ya samu ƙarin kuɗaɗen shiga da kaso 90.5, daga Naira biliyan 460 a 2023 zuwa Naira biliyan 876.5 a 2024.

Ribar da kamfanin ya samu kafin haraji ta karu da kaso 48.2 zuwa Naira biliyan 99.63 a 2024, idan aka kwatanta da Naira biliyan 67.2 biliyan a 2023. 

Sai dai asarar da kamfanin ya yi saboda canjin kuɗi ta ƙaru zuwa Naira biliyan 93.9 a 2024, daga Naira biliyan 69.9 a shekarar da ta gabace ta

By ukarofi