Gwamnati  ba ta saka hannun jari a First Bank ba – Ministan Shari’a

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ofishin Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya musanta rahotannin da ke alaƙanta Gwamnatin Tarayya da kashi 25 cikin 100 na hannun jari a bankin First Bank.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin sadarwa da yaɗa labarai, Kamarudeen Ogundele, ya bayyana labarai a matsayin “rashin gaskiya, yaudara da mugunta”.

A wani ɓangare sanarwar ta ƙara da cewa, “An tilasta mana mu mayar da martani ga wani labarin jaridar This Day na ranar 17 ga Yuli, 2025, da Arise Tɓ, wanda ke nuna cewa Gwamnatin Tarayyar Nijeriya na da hannun jarin kashi 25 a bankin First Bank.

“Gwamnatin tarayyar Nijeriya ko babban mai shari’a na tarayya da ministan shari’a ba su halarci wajen karɓar hannun jarin da ake magana a kai ba.”

Ofishin babban lauyan ya ƙara fayyace cewa ikon mallakar bankin First ya kasance mai zaman kansa ba tare da shigar gwamnatin tarayya.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Halin da ke tattare da tsarin raba hannun jari ya bambanta da duk wani sa hannun gwamnati.”

Duk da haka, ya tabbatar da cewa First Holdco ya kafa ma’aikaci, kuma babban bankin Nijeriya ya amince da Stanbic IBTC a matsayin mai kulawa na ɓangare na uku.

Fadar shugaban ƙasar ta buƙaci ƙungiyoyin yaɗa labarai da su riƙa yin “kamun kai cikin ƙwarewa, da kuma taka-tsantsan” wajen bayar da rahoton wasu batutuwa masu muhimmanci na kuɗi, tare da yin taka-tsantsan game da karya doka.

“Muna ba wa jama’a tabbacin ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da bin doka da oda, adalci, daidaito, gaskiya da kuma yi wa aasa hidima ta gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu,” inji Ogundele.

By ukarofi