Kotun Ɗaukaka Ƙara ta kori ƙarar NBC, ta jaddada haramcin tara akan gidajen yaɗa labarai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja, ta yi watsi da yunƙurin Hukumar kula da Harkokin Gidajen Yaɗa Labarai (NBC) na neman soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya na haramta mata tilasta biyan tara ga wasu gidajen rediyo da talabijin.

A wani hukuncin na tawagar alƙalai da aka gudanar a ranar Laraba, kotun ta yi watsi da buƙatar NBC, inda ta bayyana hakan a matsayin “kuskuren tsari” da “rashin fahimtar doka”.

Da take gudanar da hukuncin, Mai Shari’a Jane Inyang ta bayyana cewa yayin da shari’ar a Babbar Kotun Tarayya ake yin ta tsakanin tawagar amintattun ‘yancin gidajen jarida da NBC, an keɓance hukumar a matsayin wata gaɓar shari’ar ta daban, lamarin da ya sa ta ce Kotun Ɗaukaka Ƙarar ba ta da ikon sauraron ƙorafin.

Ɗaukaka ƙarar ta samo asali ne a ranar 17 ga Junairun 2024 yayin hukuncin Mai Shari’a Rita Ofili-Ajumogobia, inda da ta ayyana cewa NBC ta yi aiki ba bisa doka ba a lokacin da ta sanya tarar Naira miliyan biyar-biyar ga kamfanonin MultiChoice Nigeria Limited (DStv), TelCom Satellite Limited (TStv), Trust TV Network Limited da NTA StarTimes Limited a watan Agustan 2022.

NBC ta ƙaƙaba musu tarar ne bayan sun yaɗa shirye-shiryen da suka shafi ayyukan ta’addanci a Jihar Zamfara, wanda hukumat ta bayyana a matsayin cin fuska ga tsaron ƙasa.

A cewar Alƙali Rita, tarar ta saɓa wa hukuncin doka na ‘yancin yin bayani da ya haɗa da ‘yancin ‘yan ƙasa na samun labarai ba tare da shamaki ba, kamar yadda sashe na 39 na dokar ƙasa da sashe na 9 na dokar ‘yancin ɗan-adam da al’umma na Afirka suka bayyana.

Wannan hukunci ya nuna yadda shari’ar ke da ƙarfin taƙaice ikon hukumar na sanya tara akan gidajen yaɗa labarai ba tare da tsoma bakin kotu ba.

By Babaji