Kotu ta umarci NYSC ta ƙyle mata masu hidimar ƙasa su riƙa sanya siket

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Babbar kotun Tarayya da ke Abuja ta ce rashin bai wa mata masu hidimar ƙasa damar amfani da siket da hukumar NYSC ke yi ya saɓa wa doka duba da tauye ƴancin addini da hakan ke haifarwa.

A wani hukunci da Mai Shari’a Hauwa Yilwa ta gabatar a ranar 13 ga watan Yuni, 2025 ta ce dokar NYSC na amfani da wando kaɗai har ga mata ya tauye ƴancin gudanar da addini da darajar ɗan-adam.

Da fari, wasu tsofaffin ƴan hidimar ƙasa masu suna Ogunjobi Blessing da Ayuba Vivian ne suka shigar da ƙarar a takardu mabanbanta kana daga bisani Alƙali Yilwa ta haɗe su wajen yin hukunci a kai.

Daga abinda suak koka a takardun ƙarar akwai batun da ke cewa tilasta amfani da wando ya saɓa wa karantarwar addiininsu na kirista, wanda a ciki akwai haramta sanya tufafin maza ga mata.

Akan haka ne suak nemi kotun ta umarci hukumar ta soke wajabcin sanya wanda ga mata tare da barin su yin amfani siket.

A yayin hukunci kan lamarin ne kotun ta umarci NYSC da ta bar mata su riƙa sanya siket a yayin zaman a matsayin ƴan hidimar ƙasa, sannta amince da hakan a matsayin bai wa mata ƴancin gudanar da harkokin addininsu yadda ya dokar ƙasa ta sahale musu.

Haka kuma, ta umarci hukumar da ta bai ƴan hidimar ƙasar da lamarin ya shafa takardun shaidar kammala hidimarsu ta shekara guda da aka riƙe saboda sun saɓa wa dokar sanya wando.

By Babaji