Achraf Hakimi na PSG na fuskantar barazanar zuwa kurkuku kan zargin fyaɗe

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗan wasan baya na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta PSG da Moroko, Achraf Hakimi na fuskantar barazanar zuwa gidan yari na tsawon shekaru 15 bayan ɗora masa wasu zarge-zarge masu alaƙa da fyaɗe.

An fara shari’ar ne a tun a shekarar 2023.

A wata sanarwa da ƴan sandan yankin Hauts-de-Seine suka fitar, wata ƴar shekara 24 ta yi ikirarin ta haɗu da ɗan wasan ne ta manhajar Instagram.

Bayan tsawon sama da wata guda ta amince da su haɗu gaba da gaba inda ta je gidansa a garin Boulogne-Billancourt da yammacin ranar wata Juma’a.

Ta ce, ɗan wasan ne ya shirya yadda za su haɗun a lokacin da suka, sai sauya shiri daga yadda suka tsara, kamar yadda ta bayyana.

Matar ta kuma ce, Hakimi ya sumbace ta a baki da mama ta saman kayan jikinta ba tare da amincewarta ba, inda ya cigaba da shafa ta, kana daga bisani ya tilasta yin lalata da ita, lamarin da ya sa ta yi amfani da ƙarfi wajen janyewa daga jikinsa, kamar yadda ta bayyana.

Bayan ta shigar da ƙara, a ranar 3 ga watan Maris 2023 wani alƙalin bincike ya zargi ɗan wasan tareda sanya shi sahu waɗanda shari’a ta ke da tuhuma akansu.

A yayin amsa tambayoyi game da lamarin, Hakimi ya musanta baki ɗaya abinda ake tuhumar sa a kai.

By Babaji