Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke umarnin ƙwace gidaje da miliyan N400 da aka danganta da Yahaya Bello

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kotun Ɗaukaka Ƙara a Jihar Legas ta soke umarnin ƙwace kadarori 14 da kuɗi kimamin Naira miliyan 400 da aka alaƙanta su da tsohon gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello.

A wani hukunci na tawagar alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Nimpar B. Yargata, kotun ta soke hukuncin Alƙali Nicholas Oweibo na Babbar Kotun Tarayya ta Jihar, inda ta ɗaukaka ƙarar ta yi watsi da ƙarar da Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta shigar akan mallakar kuɗaɗe da kadarorin ga tshohon gwamnan.

A ranar 2 ga watan Fabarairun 2023 EFCC ta samu izinin karɓe kadarori da kuɗaɗen waɗanda ake zargin an mallake su ne ta haramtattun hanyoyi.

Daga ciki akwai wani babban gida da ke garin Burj Khalifa a Birnin Dubai na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE).

Saidai, a watan Afrilun 2023, kotun ta yi watsi da buƙatar EFCC ta ƙwace kadadorin na dindindin, saboda a cewarta Bello yana da cikakken iko a matsayinsa na gwamna a wancan lokacin na ya mallaki ababen a hukumance, kamar yadda sashe na 308 na kundin dokar ƙasa na 1999 ya bayyana.

Lamarin da EFCC’n ta bakin tawagar shari’arta ce sashen bai ba wa tshohon gwamnan ikon mallakar kadarori ta haramtattun hanyoyi ba.

Duk da haka, a yayin hukunci kan shari’ar, kotun ta ce sashen dokar bai ba kotuna damar karɓe kadarorin da ake zargin an same su ne ta haramtattun ayyuka ba ko da kuwa na gwamna ne mai ci ne.

By Babaji