Zamfara: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da sarki

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rahotanni daga Jihar Zamfara sun bayyana cewa, wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da Sarkin garin Ƴankuzo, Alhaji Babangida Kogo a jihar bayan sa’o’i da sojojin sama suka yi luguden wuta da ya yi sanadin halaka ƴan ta’adda da dama a yankin.

An ruwaito cewa, a daren ranar Talata wayewar Laraba ƴan bindigar suka yi garkuwa da shi a yankin Mararraba da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe.

Majiyoyi sun ce, lamarin ya auku ne a lokacin da Sarkin ya ke ƙoƙarin barin garin saboda tsoron kada ƴan ta’addan da suka tsira su mayar da martinin fatattakar da sojojin suka yi musu.

Wani shaida ya bayyana wa Zagazola Makama cewa dandazon ƴan bindiga da adadinsu ya kai sama da 10 da suka zo akan babura ne suka yi a awon gaba da sarkin a lokacin da ya ke tare da muƙarrabansa a kusa da wata gona da aka daina amfani da ita, wadda ta marigayi Alhaji Malami Ƴandoto ce.

Daga nan ne maharan suka tafi da sarkin tare da barin sauran waɗanda suke tare da shi.

Lamarin ya faru ne sa’o’i kaɗan da dakarun sojojin sama ƙarƙashin atisayen ‘Hadarin Daji’ suka yi wa taron ƴan ta’adda ruwan alburusai a wani jeji da ke tsakanin ƙauyukan Ƴankuzo da Munhaye.

Wani bayanin sirri ya nuna cewa, ƴan bindigar sun taru ne a wajen bikin ɗaurin aure, lamarin da ya yi sanadin halaka da dama daga cikinsu da raunata wasu.

By Babaji