Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
An bayyana cewa akwai kyakkyawar fahimta tsakanin NULGE da shugabancin ƙaramar Hukumar Ringim a Jihar Jigawa wajen aiwatar da ayyukan ci gaba a ƙaramar hukumar Ringim ƙarƙashin shugabancin Hon. Badamasi Garba Dabi, kamar yadda Alhaji Suleiman Idris ya bayyana yayin zantawa da manema labarai a makon nan.
Haka kuma ya ƙa cewa shi dai Shugaban ƙaramar Hukumar Ringim mutum ne mai kishin cigaba da son zaman lafiya wanda hakan ce ta sanya ya haɗa kai da ƙungiyoyin cigaban ma’aikata irinsu NULGE, NUT, NLC da ma sauran ƙungiyoyi da al’ummar ƙaramar hukumar Ringim bakiɗaya wanda hakan ya kawo cigaban rayuwa ta fusakar aiki da ƙarin girma na shekara-shekara a matakin ƙaramar hukuma da na JiharJigawa.
Haka zalika Kwamared Suleiman Idris ya yaba wa Gwamnan Jigawa Malam Umar Namadi ɗanmoɗi kan ƙarin albashi cikin sauƙi ba tare da kai ruwa rana ba. Saboda haka ya nemi ɗaukacin ma’aikata da jama’a su cigaba da bai wa gwamana haɗin kai da addu’a a ƙoƙanrisa na ganin ci gaban Jihar Jigawa.
Shi ma Shugaban Ma’aikatan na Rigim Abdu Sule Meza, a jawabinsa cewa ya yi ba shakaa akwai kyakkyawar fahimta tsakanin shugabancin Ringim da al’umma ƙwarai da gaske.
Shi kuwa shugaban Kansalolin Jigawa kuma Kakakin Kansilolin Ringim, Hon. Muhammad ɗanjummai Gabarin, ya ce kansu a haɗe yake da Shugaban ƙaramar Hukumar Ringim Hon. Badamasi Garba Dabi wajen aiki da burin maida ƙaramar hukumar Ringim da Jigawa kan gaba a Nijeriya.
