Gwamnonin Arewa maso Gabas sun gana da Tinubu, sun buƙaci hanyoyi da ci gaba da aikin haƙo mai a yankin

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A ranar Larabar da ta gabata ne Gwamnan Jihar BORNO, Babagana Umara Zulum, ya jagoranci takwarorinsa na shiyyar Arewa maso Gabas, zuwa wani gagarumin taro da Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda suka matsa ƙaimi wajen ɗaukar matakan gaggawa kan ababen more rayuwa da cigaba da haƙar mai a yankin.

Manhaja ta ruwaito cewa, Zulum, wanda shine shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa maso gabas, ya ce tawagar ta nemi shugaban ƙasa ya sa baki wajen kammala ayyukan tituna 17 da kuma farfaɗo da ayyukan haƙar mai a rijiyoyin kan iyaka, musamman a Kolmani da tafkin Chadi.

Daga cikin gwamnonin da suka halarci taron akwai Muhammadu Inuwa Yahaya (Gombe), Bala Muhammad (Bauchi), Mai Mala Buni (Yobe), Ahmadu Umaru Fintiri (Adamawa), da Agbu Kefas (Taraba).

Zulum ya lissafo muhimman hanyoyin da ke buƙatar kulawar gwamnatin tarayya, da suka haɗa da titin Kano – Maiduguri, titin Bama – Mubi – Yola, titin Wukari – Jalingo – Yola, titin Bauchi – Gombe – Biu – Damaturu, da titin Maiduguri – Monguno – Baga.

Ya kuma buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ba da fifiko kan layin dogo na Fatakwal – Jos – Bauchi – Maiduguri, wanda ya bayyana da cewa yana da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa kasuwancin yankin.

Gwamnan ya yaba da ƙoƙarin da Shugaba Tinubu ya yi na tabbatar da zaman lafiya a yankin da kuma ci gaba da ayyukan yaƙi da ta’addanci.

“Muna gode muku don samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin yankin da kuma ci gaba da yunƙurin magabata na ci gaba da yaƙi da masu tayar da ƙayar baya,” inji Zulum.

Ya sake tabbatar da goyon bayan gwamnonin ga “Ajenda Renewed Hope” na Tinubu, tare da yin alƙawarin yin aiki tare da ƙoƙarin tarayya na ƙarfafa horar da ma’aikata, tura fasaha don magance rashin tsaro, da kuma inganta ci gaban noma.

A nasa martanin, Shugaba Tinubu ya amince da ƙorafin da suka kawo, ya kuma ba tawagar tabbacin aniyar gwamnatinsa na ganin ta magance da buƙatun ci gaban yankin.

By ukarofi