Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Sanatan Kano ta Tsakiya Hon. Rufa’i Sani Hanga ya ƙaddamar da aikin yin wata sabuwar hanya mai tsawon kilomita 300 a mazaɓar Gobirawa a yankin ƙaramar Hukumar Dala.
Sanatan ya yi kira ga al’ummar yankin kan su baiwa ma’aikata da za su yi aikin cikakken goyon baya da haɗin kai a yayin da suke gudanar da aikin.
Sanata Rufa’i Sani Hanta ya ce alummar yankin ne suka zo masa da buƙatar a yi wannan aikin ba hanya ya gode wa Allah da ya bashi dama ya zo don ƙaddamar da aikin yana fatan Allah ya yi masa jagora akai.
A jawabinsa shugaban ƙaramar hukumar Dala Hon. Suraj Imam ya ja hankalin ɗan kwangila da zai gudanar da aikin ya yi mai inganci kuma ya san duk aikin da Sanata Rufa’i Hanga zai bayar mai ƙwari ne kuma yana biyan ɗan kwangila akan lokaci.
A nasa ɓangaren shugaban jam’iyyar NNPP na ƙaramar hukumar Dala, Alhaji Dayyabu Ahmad Mai Turare ya bayyana cewa, suna maraba da irin ayyuka da Sanatan Kano ta tsakiya Rufa’i Sani Hanga yake musu, kama daga gina makarantu da tituna da tallafawa matasa ta horar da su sana’o’i da ba su jari a ɓangarori na sana’o’i daban da shi ma shaida ne akai.
Da yake zantawa da yan jarida.babban hadimi na musamman ga Sanatan Kano ta tsakiya, Hon. Nura Mai ƙarfi Dala ya bayyana farin cikinsa bisa wannan muhimmin aiki da Sanata Rufa’i Sani Hanga ya kawo Gobirawa da al’ummar yankin suke da matuƙar buƙatarsa.
Ya ce kawo aikin titin shaida ce akan jagoransu Sanata Rufa’i Sani Hanga mai sauraren buƙatun al’umma ne,domin jama’ar yankin su suka je masa da buƙatar a yi titin kuma ya amsa musu ga shi har an zo an ƙaddamar da soma yinsa.
Ya ƙara da cewa ba wannan kaɗai ba, al’umma shaida ne akan irin ɗinbin ayyuka da Sanatan Kano ta tsakiya ya kawo ƙaramar hukumar ta Dala kama daga gina makarantu da horar da matasa maza da mata akan sana’o’i da ba su jari da aikin kula da lafiyar al’umma da kuma tallafawa harkar cigaban ilimi da sauran abubuwa da yawa.
Hon. Nura Mai ƙarfi Dala ya ce irin wannan tagomashi na ayyuka da kulawa da jama’a haka Sanata Rufa’i Sani Hanga yake a dukkan ƙananan hukumomi da suke ƙarƙashin mazaɓun Kano ta tsakiya har ma yana kawo ayyuka da za su amfani al’ummar jihar Kano gaba ɗaya.
