Abinda ya sa na zaɓi zaman lafiya akan siyasa – Fubara kan dokar ta-ɓacin Ribas

Spread the love

Gwamnan jihar Ribas Siminalayi Fubara ya bayyana cewa saboda buƙatar zaman lafiya ya sa bai ƙalubalanci ayyana dokar ta-ɓaci ba a jiharsa, wanda hakan ya yi sanadin dakatar da gwamnatinsa na tsawon wata shida.

A watan Maris Shugaba Bola Tinubu ya sa dokar, wadda ta ƙare a ranar Larabar da ta gabata, lamarin da ya dawo da gwamnan da majalisar dokokin jihar bakin aiki.

Da yake jawabi ta kafar talabijin, Siminalayi Fubara, ya ce zai fuskanci lamuran mulki ne don cigaba ta hanyar shimfiɗa ayyukan raya ƙasa da zaman lafiya tsakaninsa da sauran zaɓaɓɓun jami’an gwamnati.

Fubara ya kuma yaba wa Shugaba Tinubu kan sulhunta tsakanin sa da tsohon gwamnan jihar kuma Ministan Abuja Nyesom Wike da suka yi ta samun rashin jituwa a siyasa.

Kazalika ya buƙaci al’ummar jihar da su ɗauki matakin juriya domin jihar ta shiga mawuyacin hali a lokacin dokar ta-ɓacin.

By Babaji