Daga USMAN KAROFI a Abuja
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa matsalolin tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta sakamakon wasu sauye-sauyen da gwamnatinsa ta aiwatarwa ne. Ya bayyana cewa wannan yanayi ya damu ne saboda tiyata da gwamnatin sa ke yi wa tattalin arzikin ƙasar.Tinubu ya ce wannan wahala da ake ciki ba za ta dawwama ba domin tattalin arzikin ƙasar ya fara murmurewa daga matsalolin da ya faɗa, inda ya gode wa ‘yan ƙasa bisa haƙuri da juriyar da suka nuna.
Tinubu ya yi wannan bayani ne a ɗakin taro na Mapo Hall dake Ibadan, Jihar Oyo, a lokacin bikin naɗa sabon Olubadan na Ibadan, Oba Rashidi Adewolu Ladoja, wanda shi ne sarki na 44 a jerin sarakunan garin. Ya bayyana cewa akwai haske a ƙarshen rami, inda ya buƙaci al’umma da su ƙara hakuri saboda nan gaba kusa za a ga sakamakon ci gaba da bunƙasa.
Bikin naɗin sarki Ladoja ya samu halartar manyan baƙi da dama ciki har da gwamnoni, ministoci da kuma sarakuna daga sassa daban-daban na kasar. Daga cikin waɗanda suka halarta akwai gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, da gwamnonin Ondo, Osun, da Ekiti. Haka kuma, Sultan na Sokoto, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, da Alaafin na Oyo, da sauran sarakuna na gargajiya sun halarci bikin.
Oba Ladoja ya gaji marigayi Oba Owolabi Olakulehin wanda ya rasu a ranar 7 ga Yuli, 2025, bayan shekara ɗaya kacal a kan karagar mulki. Sabon sarkin ya hau karagar mulki ne kusan watanni uku bayan rasuwar wanda ya gada, lamarin da ya sanya wannan biki zama tarihi ga al’ummar Ibadan da ma Najeriya baki ɗaya.
