Gwamnatin Katsina ta raba tallafi ga mutane 600 da ambaliya ta shafa a Kankiya

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugabar hukumar agajin gaggawa SEMA Hajiya Binta Hussaini Dangani ta jagorancin ƙaddamar da raba kayan tallafin a ƙaramar hukumar Kankya.

Kayan tallafin ya haɗa da nau’in abinci da kuma kayan kwanciya gami da sauran kayan amfanin yau da kullum, da suka haɗa da, shinkafa, masara, gero, dawa, katifa, tabarma, bargo, magi, gishiri da kuma man gyada.

Da ta ke gabatar da jawabinta yayin da ta ke ƙaddamar da tallafin, shugabar hukumar Haj. Binta Husaini Dangani ta bayyana cewa tallafin ya samu ne bisa umarnin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa domin a rage raɗaɗi ga mutanen da iftala’in ya shafa.

Taron raba tallafin ya samu halartar shugaban ƙaramar hukumar Kankiya Hon.Lawal Abdullahi Gezi wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Hon.Ashiru Hamisu Magam, tare da wakilin hakimin Kankiya, kansiloli da sauransu.

By ukarofi