Zargin auren dole: Iyali sun wanke Sarkin Mafara tare da neman afuwarsa

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Mahaifan Maryam wadda tun da farko ita da Mahaifiyarta suka zargi Sarkin Talatan Mafara, Dakta Bello Mohammed Barmo a Kihar Zamfara da yin amfani da ƙarfin ikon sa wajen aurar da Maryam ga wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Mi’awiyya sun wanke Basaraken daga zargin da suka yi masa cewar yana da hannu a kan lamarin.

Malam Umar Musa wanda kawun Maryam ne ya jagoranci tawagar Iyalan zuwa fadar Sarkin a yau ranar Talata ya bayyana hakan a gaban Sarkin.

A cewarsa, sun je fadar Sarkin ne domin su wanke shi da zargin da Mahaifiyar Maryam da ita kanta Maryam su kayi masu suna masu neman gafarar sa kan yunƙurin ɓata masa suna daga ‘yarsu da Mahaifiyar ta su ka yi masa.

A farkon wannan shekarar ne Maryam da mahaifiyar ta Hafsat Shehu suka zargi fadar Sarkin Mafara Dr. Bello Mohammed Barmo da tilastawa Maryam auren dole wanda ya ja hankalin ƙungiyar kare hakkin bil’adama.

Malam Musa ya bayyana abin da ya faru tsakanin ‘yar su da masarautar Mafara a matsayin abin takaici, mara tushe balle makama.

Ya kuma yi kira ga Sarkin da ya gafarta wa iyalan su baki ɗaya, ganin cewa ita ce kadai mafita ga abin da ya faru.

“Munzo wannan fada mai daraja a ƙarƙashin jagorancin Sarkin Mafara, Dakta Bello Mohammed Barmo domin neman gafarar sa kan abin da ‘yarmu da mahaifiyar ta suka yi masa, kuma mun yi imani da hakan aikin sheɗan ne. Yace

Da yake mayar da martani, Sarkin Mafara, Dokta Bello Mohammed Barmo ya bayyana farin cikinsa da wannan mataki da suka ɗauka.

Sarkin ya bayyana cewa masarautar sa ba ta taɓa sa baki a duk wani lamari na auren dole a tsakanin waɗanda abin ya shafa ba, yana mai bayyana abin da ya faru a matsayin yunƙurin ɓata sunan shi da masarautar.

Daga ƙarshe Dr. Barmo ya yafewa Maryam da Mahaifiyarta Hafsat Shehu da ɗaukacin ‘yan uwan su a kan abinda ya faru.

“A matsayina na musulmi, dole ne in rungumi ƙaddara mai kyau ko mara kyau, kuma na gafarta ma duk wanda ya ɓata min Suna dangane da wannan lamarin.

Ya kuma yi kira ga iyaye a masarautar sa da su riƙa amincewa da duk wanda ‘yar su ta kawo a matsayin wanda takeso ta aura domin gujewa rikici.

A cewarsa, aure bana wucin gadi ba ne amma wani abun ne rayuwa dindindin, don haka akwai buƙatar iyaye su yi taka tsantsan ta hanyar amincewa da duk wanda ‘ya’yansu mata suka gabatar, shi suke so su aura domin a samu zaman lafiya.

By ukarofi