
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mai Shari’a Mohammed Umar na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ya ƙi amince wa buƙatar bada belin wanda ake zargi da shiga tsakani da ƴan bindiga, wato Tukur Mamu.
A yayin sauraron ƙarar a yau Laraba, Alƙalin ya ce ƙorafin da aka shigar a matsayin dalilin neman belin, wanda shi ne halin lafiyar wanda ake ƙara bai gamsar da kotun ba.
Saidai, a madadin haka ya umarci hukumar da ke tsare da shi, wato DSS da ta kai shi asibitin da ya dace da halin da yake ciki.
Haka kuma, Alƙalin ya bayyana cewa duba da yadda aka ɗauko shari’ar Mamu tun da fari, tawagar da ke aiki akan batun na iya ƙoƙarinta wajen ganin ta yi abinda ya dace cikin kulawa da wanda aka tsare akan tuhumar.
Don haka, ana yin beli ne a yayin da aka samu gazawa ta ɓangaren waɗanda ke kula da wanda aka tsare, lamarin da ya hana samun belin, kamar yadda Mai Shari’ar ya bayyana.
Sannan, ya umarci DSS ta ba Tukur Mamu damar ganawa da iyalansa.
