An gano dalilan da suka kawo jinkirin daƙile yaɗuwar cutar mashaƙo Bichi

Spread the love

Daga USMAN NASIR KAROFI a Abuja

An gano dalilan da suka taka rawar gani wajen jinkirin daƙile yaɗuwar cutar mashaƙo a ƙaramar hukumar Bichi, bisa baƙunci na wakilai masu ruwa da tsaki a fannin daga matakin jiha, ƙasa tare da wasu wakilai na manyan ƙungiyoyin da suka shafi harkokin lafiya na duniya.An gano dalilan da suka taka rawar gani wajen jinkirin daƙile yaɗuwar cutar mashaƙo a ƙaramar hukumar Bichi, bisa baƙunci na wakilai masu ruwa da tsaki a fannin daga matakin jiha, ƙasa tare da wasu wakilai na manyan ƙungiyoyin da suka shafi harkokin lafiya na duniya.

A sanarwar da jami’ar yaɗa labarai ta ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta fitar, wakilan masu ruwa da tsaki a harkokin lafiya sun ce mutane 726 ne suka kamu da cutar a ƙaramar hukumar Bichi.

Wakilan, ƙarkashin jagorancin shugaban hukumar yaƙi da cututtuka ta ƙasa (NCDC), Dk. Muzammil Gadanya sun ziyarci asibitoci da al’umar da ke cikin gari da cikin gidaje, musamman yankin da cutar ta yawaita kamar garuruwan Kaukau, Agata, Rimayen Rake, Buden Gari, Tafkin Bako da Badume.

Sun fahimci cewa cutar ta yaɗu ne sakamakon baƙi daga wasu jihohi da kuma yara almajirai da ake kai wa karatu wasu garuruwa daban da ake dawowa da su gida bisa larurar rashin lafiya ta zazzaɓi ko ciwon kai, wanda daga baya ma’aikatan lafiya ke gano cewa cutar mashaƙo suka kamu da ita. Kazalika, binciken tawagar ya bayyana cewa wasu jama’ar yankin ba sa kai ‘ya’yansu rigakafin da aka saba yi wa yara daga matakin haihuwa zuwa shekara biyu, sun fi karkata ga maganin gargajiya ka’in da na’in.

“Mutane yawanci suna jahiltar abin da ba su fahimta ba ne, don haka mu ci gaba,da abin da muke yi na wayar da kan al’uma.” Dr. Muzammil Gadanya.

Tawagar da ta haɗar da; Shugabar rigakafi ta Kano, Hajiya Sa’adatu Ibrahim, Shugaban binciken cututtuka masu yaɗuwa na jiha, Dakta Babangida Saleh Ibrahim, jami’in binciken lafiya na jiha, Muslim Shehu Kafinta, wakilin ƙungiyar ba da tallafi a kan harkokin lafiya, Malam Lawan Gambo da wakiliyar hukumar yaƙi da cututtuka (NCDC) ta ƙasa, Peace Umar da wakiliyar kula da Lafiya ta duniya, Juliana A Kudu, wakilan sun zauna da wakilan masarauta da suka haɗar da; sakataren Hakimin Bichi, Galadiman Kano, Alhaji Mannir Sanusi, Malam Shitu Malikawa tare da dagatai da masu unguwanni domin cimma nasara, da kuma wakilan ƙaramar hukumar Bichi ciki har da Kansilar Lafiya Bashir Sabi’u Saye, wanda yayi magana a madadin shugaban ƙaramar hukumar, Alhaji Hamza Sule Maifata.

“Ƙaramar hukuma za ta sayi magunguna ta ajiye, kuma za ta ci gaba da sa ido a kan wannan domin mu ga yadda ƙaramar hukuma za ta tallafa a kan waɗannan matsalolin da suke faruwa.” In ji shi.
 
A ƙoƙarin kawar da cutar baki ɗaya, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, wakilan gwamnatin, da suka hadar da; Shugabar rigakafi ta Kano, Sa’adatu Ibrahim, Shugaban binciken cututtuka masu yaɗuwa na jiha, Dakta Babangida Saleh Ibrahim, jami’in Binciken lafiya na jiha, Muslim Shehu Kafinta, wakilin ƙungiyar ba da tallafi a kan harkokin lafiya, Malam Lawan Gambo, sai kuma wakilan ƙasa; Dr Muzammil Gadanya, Shugaban hukumar NCDC ta ƙasa, Juliana A Kudu, wakiliyar hukumar kula da lafiya ta duniya da kuma wakiliyar (NCDC) ta ƙasa, Peace Umar.

By ukarofi