
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Litinin Shugaba Bola Tinubu ke wata ganawar sirri da sababbin jagororin tsaro a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
An fara zaman ne tun da tsakar rana, saidai ba san asalin abinda ake tattaunawa a kai ba, amma majiyoyi sun ce bai rasa nasaba da ƙoƙarin da gwamnatin tarayya ke yi wajen inganta harkokin tsaro musamman duba da yadda fannin ya ke samun sabbin ƙalubale.
A kwanan nan Fadar ta fitar da sanarwar cewa garambawul da Shugaba Tinubu ya yi wa fannin tsaro musamman rundunar sojoji, dabar ce ta inganta ƙwarewa da samar da kyawawan sakamako a fannin.
Waɗanda suka halarci zaman sun haɗa da Babban Hafsan Tsaro, Janar Olufemi Oluyede; Shugab sojoji, Manjo Janar Waidi Shaibu; Shugaban sojojin sama, Air Vice Marshal Kennedy Aneke; da Shugaban Sojin ruwa, Rear Admiral Idi Abbas.
