Wani labari mai taɓa zuciya ya karaɗe kafafen sada zumunta bayan wata mata ta ruwaito yadda ta samu ’yan tagwaye bayan shekaru kimanin 10 tana fama da rashin haihuwa.
Matar, wadda ta kasance cikin auren farko na tsawon shekaru goma ba tare da ta samu haihuwa ba, ta sha gwaje-gwaje da jinyoyi ciki har da zagaye biyar na IɓF da duk suka gaza. A ƙarshe, ta yanke shawarar daina gwaje-gwajen, ta kuma mayar da hankali kan rayuwarta ba tare da matsin lambar neman ciki ba.
Sai dai yayin da ta ke ci gaba da gwagwarmaya, auren nata ya mutu ta hanyar saki. Bayan shekara guda ta sake samun sabuwar soyayya, ta kuma yi aure. A wannan karon, ba tare da wani magani ko gwaji ba, ta sami abin mamaki — ta yi ciki, kuma haifi tagwaye.
Ta wallafa hotunan cikinta tana cike da farin ciki da godiya yayin da ta ke shirye da haihuwa, inda ta ce “komai ya fara sauyawa bayan na haɗu da masoyin rayuwata.”
A kwanakin baya, ta sanar da haihuwar ‘yan tagwayenta, tana bayyana su a matsayin “soyayyata ta gaskiya.”
Labarinta ya bazu sosai a intanet, inda mutane da dama suka taya ta murna, suna cewa wannan hujja ce mai ƙarfi ta imani, fatan alheri da lokacin Allah — cewa mu’ujizai kan faru ne a lokacin da ba a zata ba.
