Magidanci ya ɓarke da kuka bayan matarsa ta haifi ’yan shida

Spread the love

Wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna wani mutum yana kuka sosai a asibiti bayan matarsa ta haifi ‘ya’ya shida lokaci guda.

Rahotanni sun ce matar ta haifi jarirai shida a lokaci ɗaya, abin da mijin bai taɓa zato ba.

A maimakon farin ciki da yawanci ake yi a irin wannan lokaci, mutumin, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya fashe da kuka a gefen jariran, yana bayyana damuwarsa kan yadda za su kula da su a irin wannan mawuyacin halin tattalin arziki.

A cikin bidiyon, an jiyo shi yana faɗa wa matarsa da mamaki, “Kin samu aarfin zuciya kika haifi ’ya’ya shida a wannan lokaci?”

Ma’aikatan jinya a asibitin sun yi ƙoƙarin lallashi da kwantar masa da hankali, suna gaya masa cewa yara alheri ne daga Allah, kuma Allah ne zai ba su ikon kula da su. Amma duk da haka, mutumin ya ci gaba da kuka, yana nuna rashin yarda da halin da suka tsinci kansu a ciki.

A ɓangaren jama’a kuwa, masu amfani da kafafen sada zumunta sun raba ra’ayoyinsu – wasu suna ganin kukan nasa ya nuna tsoron nauyin kula da yara da yawa a lokaci guda, yayin da wasu suka ce kamata ya yi ya nuna godiya ga Allah bisa wannan babban alheri.

Wasu masu sharhi sun rubuta cewa, “Ko da yake yana da wahala, amma wannan kyauta ce daga Allah da ba kowa ke samu ba.”

An ruwaito cewa jariran shida da mahaifiyarsu suna cikin ƙoshin lafiya bayan haihuwar da ta faru a wani asibiti a Nijeriya.

By ukarofi